Tsarin tekunan duniya da abubuwan da ke cikinsu (4)

MatashiyaWatanni uku da suka gabata mun fara silsila kan tekunan duniya da yanayinsu da irin abubuwan da suke dauke dasu na amfanin dana dam.  Mun dakata a kan bayanin tekun Pacific ne, wato teku na farko kuma mafi girma a duniya kenan.  Kamar yadda bayani ya gabata a baya, dukkan tekun nan na duniya asalinsu […]

Tsarin tekunan duniya da abubuwan da ke cikinsu (4)

Matashiya
Watanni uku da suka gabata mun fara silsila kan tekunan duniya da yanayinsu da irin abubuwan da suke dauke dasu na amfanin dana dam.  Mun dakata a kan bayanin tekun Pacific ne, wato teku na farko kuma mafi girma a duniya kenan.  Kamar yadda bayani ya gabata a baya, dukkan tekun nan na duniya asalinsu teku ne guda daya.  Dalilin rabuwarsu dai ko karkasuwansu bai rasa alaka da bigiren da bangaren tekun yake, da irin nahiyoyin da yake makwabtaka da su, da tsibiran da ke cikinsa.  Hakan ne ya sa aka samu rarrabuwa.  A yau cikin yardar Ubangiji, bayan wani lokaci da muka kwashe muna tattaunawa kan tsarin mu’amala da Password da ka’idojinsa, mun sake dawowa don ci gaba da bayani kan tekunan duniya.  Za mu tashi da bayani kan teku na biyu wajen girma a duniya, wato Tekun Atlantika (Atlantic Ocean).

Tekun Atlantika
(Atlantic Ocean)
Tekun Atlantika, ko “Atlantic Ocean” kamar yadda ake ambatonsa a harshen Turanci, ko kuma “Tekun Legas” kamar yadda a al’ada muke kiransa a kasarmu, shi ne teku na biyu wajen girma a duniya, bayan tekun Pacific da bayaninsa ya gabata a baya.  kalmar “Atlantic” da ake danganta wannan tekun da ita dai ta samo asali ne daga kalmar “Atlas” wanda asali sunan wani ne daga cikin shahararrun mutanen tsohuwar Daular Romawa.  Daga sunansa ne ake danganta wannan teku.  Bayan nan, a bangaren gabashin Afirka kuma a baya ana kiran wannan teku ne da suna: “Ethiopian Ocean,” wato “Tekun Habasha.”  To amma bayan wasu lokuta sai aka tabbatar da suna guda don ishara ga wannan teku, wato: “Atlantic Ocean,” kamar yadda muke ambatonsa da shi yanzu.
Wannan teku, idan aka yi la’akari da girmansa, ya kai kashi daya cikin biyar (1/5) na fadin duniya baki daya, wato kashi ashirin kenan cikin dari (20%).  Ta bangaren yawan ruwa kuma, idan aka tara ruwan duniya, tsakanin wanda ke tekuna da wanda ke koguna da rafuka da gulabu, kashi ashirin da tara (29%) na cikin tekun Atlantika ne.
Wajen fadi a iya haddinsa, Tekun Atlantika ya kai fadin murabba’in kilomita miliyan dari da shida da dubu dari hudu (106,400,000 skkm) idan aka yi la’akari yawan ruwan da ke kwararo masa daga cikin kananan kogunan da ke harabarsa kenan.  Shi ne tekun da ya mamaye fadin ilahirin inda ya faro zuwa karshensa, a siffar harafin “S”.  Ma’ana, idan ka hango Tekun Atlantika daga sararin samaniya, za ka gan shi ne a siffar babban harafin “S”.  Shi ya sa wasu masana idan aka tambaye su, shin, wane teku ne Tekun Atlantika?  Sai su ce: “Tekun da ya mamaye mahallin kasa a siffar harafin “S”, daga nahiyar Turai-maso-Asiya (Eurasia) zuwa nahiyar Afirka.”

Makwabta
Kamar yadda tekun Pacific ya yi makwabtaka da wasu kasashe ko nahiyoyi na duniya, haka ma Tekun Atlantika ya yi.  Dalili kuwa shi ne, yana daya daga cikin bangarorin tekun duniya baki dayansa, tun da asalinsu daya ne.
Ta bangaren arewacinsa, Tekun Atlantika yana makwabtaka ne da tekun Aktic (Arctic Ocean). Ta bangaren Kudu maso Yamma kuma, ya yi makwabtaka ne da babban tekun duniya, wato Tekun Pacific.  A bangaren kudu maso gabas kuma, akwai Tekun Maliya (Indian Ocean).  A bangaren kudu tsantsa kuma, Tekun Atlantika na makwabtaka ne da Tekun Kudancin duniya, wato Southern Ocean.
Idan aka dunkule Tekun Atlantika gaba dayansa kamar yadda yake a taswirar duniya, Kambun duniya (Ekuator) ya raba shi zuwa bangarori biyu ne.  bangaren farko shi ne bangaren Arewaci, wanda ake kira da suna: “North Atlantic Ocean.”  Sai bangare na biyu mai suna: “South Atlantic Ocean.”  Bayan wadannan bangarori guda biyu, masana sun kara cewa akwai bangaren tsakiya da suka kira: “Central Atlantic Ocean.”  Wannan shi ne bigiren dake tsakanin nahiyar Kudancin Amurka (South/Latin America) da nahiyar Afirka.  Suka ce nau’in dabi’ar ruwa dake bigiren tsakiya ya sha bamban da wanda ke Arewacin Amurka da Turai (America & Europe).
A jumlace dai, Tekun Atlantika na jingine ne a kirjin nahiyar Arewaci da Kudancin Amurka, ta bangaren yamma kenan.  A nan ne ya hade da Tekun Aktik da ke makurar arewaci, ta hanyar kananan kogunan da ke harabarsa, irin su: Kogin Denmak, da Kogin Greenland, da Kogin Norway, sai kuma Kogin Barents.
A bangaren gabashin duniya kuma Tekun Atlantika na fuskantar nahiyar Turai ne, inda ya hade da Kogin Dutsen Taarik (Jabalu Taarik, ko Gibraltar), wanda shi ne mahadin kogin (Strait) da ya hada alaka tsakanin Tekun Atlantika da babban Kogin Meditaraniyan (Mediteranian Sea).

Girma da Fadi
Idan ka cire kananan koguna da ke kwararo masa ruwa, fadin Tekun Atlantika ya kai murabba’in kilomita (Skuare Kilometers) miliyan tamanin da biyu da dubu dari shida (82,600,000 skkm).  Yawan ruwan dake dauke a cikinsa kuma ya kai mizanin miliyan dari uku da ashirin da uku da dubu dari shida (323,600,000 cubic meters) a ma’aunin cubic.  Idan ka hade da yawan ruwan dake kananan kogunan da ke harabarsa kuma, yawansu ya kai miliyan dari uku da hamsin da hudu da dubu dari bakwai (354,700,000 cubic meters) a ma’aunin cubic.
Tekun Atlantika ne tekun da ya fi kowane teku  samun ruwa masu shigo masa daga wasu koguna da ke habara ko makwabtaka dashi.  Domin nahiyoyin duniya da yake kusa da su suna samansa ne.  Wannan ya sa duk wani kogi da ke makale da su, ruwansa ke kwararowa zuwa cikinsa kai tsaye.  Shahararrun kogunan da ruwansu ke kwararowa zuwa Tekun Atlantika kai tsaye sun hada da: Kogin tsibirin St. Lawrence, da Kogin Mississipi, da Kogin Orinoco, da Kogin Amazon da ke Burazil, da Kogin Rio de la Plata shi ma a Burazil, sai Kogin Congo, da Kogin Naija da ke kasarmu Najeriya, da Kogin Loire, da Kogin Rhine, sai kuma Kogin Elbe.  Dukkan wadannan koguna ruwansu na kwarara ne cikin Tekun Atlantika kai tsaye.  A duniya babu tekun da ke samun ta wannan hanya irin Tekun Atlantika.

Zurfi
A bangaren zurfi kuma, Tekun Atlantika yana da zurfi irin nashi, duk da cewa bai kai Tekun Pacific ba.  Mahalli ko bigiren da ke da matsakaicin zurfi a cikinsa ya kai zurfin mita dubu uku da dari tara a shirin da shida (3,926 meters).  Bigire mafi zurfi a Tekun Atlantika shi ne mai zurfin mita dubu takwas da dari uku da tamanin (8,380 meters), wanda ya yi daidai da taku dubu ashirin da bakwai da dari hudu da casa’in kenan (27,490 feets).  Wannan bigire da ya fi zurfi a Tekun Atlantika shi ake kira: “Milwaukee Deep,” kuma yana daidai Tsibirin Puerto Rico ne, can wajen Kudancin Amurka kenan.

dandano da dabi’ar Ruwa
Abu ne sananne cewa ruwan ya sha bamban da sauran nau’ukan ruwa wajen dandano.  A yayin ruwan sama da na kogi da na rafi da gulbi suke da gardi wajen dandano, ruwan teku yana da zartsi ne, wato dandanon gishiri kenan.  Binciken malaman kimiyya ya tabbatar da cewa Tekun Atlantika shi ne teku mafi zartsi a duniya.  Ma’ana, darajar dandanon gishiri da ke cikin ruwansa ya fi na sauran tekunan duniya sosai.  An kuma kiyasta cewa darajar zartsin da ke cikin ruwansa ya fi na sauran da daraja 3.3 zuwa 3.7.
Manyan dalilan da suka sa ruwan Tekun Atlantika ya fi sauran wajen dandano da zartsi, a cewar masana, sun hada da: yawan tururin iska da ke haurawa zuwa sararin samaniya daga kan tekun.  Dalili na biyu shi ne yawaitar ruwan da ke shigowa cikinsa daga wasu kananan koguna da ke makwabtaka da shi, kamar yadda bayani ya gabata a baya.  Dalili na uku shi ne, kankarar da ke narkewa daga jikin tsaunukan kankara da ke cikin tekun.  Wadannan tsaunukan kankana su ake kira “Glaciers.”
A daya bangaren kuma, bigiren da ruwansa ya fi karancin zartsi a tekun gaba daya shi ne bangaren Arewacinsa, wato: “North Atlantic.”  Masana suka ce babban dalilin karancin zartsinsa shi ne yawaitan ruwan sama da ake samu a bangaren, wanda ke kwarara cikin tekun.