Tsarin tsaron Gwamna Shema zai kai ga nasara
Talakawan Jihar Katsina ya kamata su hada karfi wajen tabbatar da cin nasarar dabarun tsaro da Gwamnatin Ibrahim Shema ta bullo da su a a Jihar Katsina, tsarin tsaro, wanda in har aka ba shi muhimmanci ,ba karamar fa’ida za a samu a kasa ba. Domin a tsari ne da gwamna ya yi nuni da […]
Talakawan Jihar Katsina ya kamata su hada karfi wajen tabbatar da cin nasarar dabarun tsaro da Gwamnatin Ibrahim Shema ta bullo da su a a Jihar Katsina, tsarin tsaro, wanda in har aka ba shi muhimmanci ,ba karamar fa’ida za a samu a kasa ba. Domin a tsari ne da gwamna ya yi nuni da cewa ba lallai sai an baza jami’an tsaro za a hana al’umma aikata ta’addanci ba, musamman idan aka samar wa matasa ayyukan yi; aka wadata kasa da wutar lantarki; aka bunkasa aikin gona; aka hana tu’amalli da miyagun kwayoyi; sannan aka yi kokarin shawo kan miyagun laifukan da ake tafkawa a kan iyakokin kasar nan.
Wani babban abin farin ciki da ke kunshe a cikin tsarin tsaron Gwamna Shema, shi ne yadda yake kokarin hada karfin Shugabannin al’umma, wadanda suka hada da Sarakunan Gargajiya da Malaman Addini da shugabannin Siyasa da daidaikun mutane, wadanda ke da gagarumar gudunmuwar da za su bayar don kawar da matsalolin da ke ci wa al’umma tuwo a kwarya.
Sanin kowa ne Gwamna Ibrahim Shema ya taba nuna takaicinsa kan yadda har yanzu ba a ceto ’yan matan Chibok ba, musamman idan an yi la’akari da cewa hare-haren kunar bakin wake rashin aikin yi ne da rashin wutar lantarki da shan miyagun kwayoyi da miyagun ayyukan da ake tafkawa a kan iyakokinmu (Shema, jaridar Turanci ta The Sun, 2 ga watan Yulin 2014).
Da zarar manomanmu suka dore da samun tallafi irin na Gwamnatin Shema, tabbas Jihar Katsina sai ta ciyar da kasar nan.Kuma idan har matasa suka rungumi noma, babu ta yadda za a yi kowa yace sai ya yi aikin gwamnati; uwa-uba za a daina samun masu zaman kashe wando.
A duk lokacin da Shugabannin al’umma suka tabbatar suna da nauyin da ya kamata su sauke, don kyautata rayuwar kowane mutum da hakkin ba shi kariya ta raya a kansu, to kowace irin matsalar rayuwa ta bijiro wa mutane a kan samu sassauci. Don haka mu a Jihar Katsina, ya zama dole ga malaman addini su dora mutane kan tafarkin da zai hana miyagu su yi amfani da su wajen ayyukan ta’addanci, musamman in an yi la’akari da halin da matasa ke ciki. Shugabannin Siyasa, tun daga matakin kananan hukumomi su jajirce wajen aiwatar da ayyukan da za su kyautata rayuwar al’umma, musamman aikin gona, a rani da damin don hana matasa kwararowa cikin birni neman abin da babu. Su kuwa sarakunan gargajiya, ya zama wajibi su tsawatar a kan duk wasu tsiyataku da suka hango batagari na yunkurin jeho su cikin al’umma. Idan ka samu wannan, lallai daidaikun mutane za su kasance masu in doka da oda.
Tunda a ciki da wajen Jihar Katsina muna da dimbin masana ’yan asalin wannan jiha, ina ganin akwai bukatar su tallafa wa tsarin Gwmana Shema na tabbatar da tsaron dukiya da rayuwar al’umma jihar nan, musamman ta hanyar amfani da iliminsu don bullo da dabarun samar da ayyukan yi. Kai hatta hamshakan ’yan kasuwa, ya kamata su suka jari wajen samar da wutar lantarki, don kada a bar gwamnati ita kadai tana ta fafutika. Wannan ne ma dalilin da ya sanya, wata sa’a masu sukar gwamnati ke fakewa da cewa ba ta aiki. To ni dai na san cewa, “Hannu daya ba ya daukar jinka,” a cewar Malam Bahaushe.
Tunda Gwamnatin Jihar Katsina ta fito da tsarin kula da lafiya na tafi-da-gidanka, me zai hana malaman makaranta su, ko wani gungu na masana su bullo da tsarin ilimantar da al’umma na tafi-da-gidanka ba? Me zai hana a samu wasu ’yan kasuwa daga jihar nan da za su bullo da tsarin-kasuwanci na tafi-da-gidanka ba? Me zai hana a samar da masu sa’ido kan harkokin tsaro na tafi-da-gidanka ba?
Matukar al’ummar Jihar Katsina suka bayar da amsar wadannan tambayoyi da na bijiro da su, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko akidar addini ko bangaranci ba, tabbas sai jiharmu tafifita a kan sauran jihohi; kuma jihar za ta zama abin koyi ga kowace jiha da ke fadin kasar nan.
Shi kuwa Gwamna Shema, tunda a tsaye yake wajen ganin dabarun tsaro da ya bullo da su sun samu kai ga nasara, akwai bukatar ya kara kaimi, wajen jawo daidaiku da kungiyoyin al’umma da za su taimaka don kai ga nasara. Wannan kuwa ya zama wajibi tunda Malam Bahaushe ya ce, “Idan kana da kyau, to kara da wanka.”
Da zarar mutanen Katsina sun fahimci manufofin Gwamnatin Shema, musamman dabarun tsaro, babu yadda za a yi matashin da ke da aikin yi ya yarda wani ya yi amfani da shi ta hanyar da ba ta dace ba. Kai hasali ma yadda ake kokarin habaka noma da kiwo a Jihar Katsina, idan aka kai ga nasara da wuya kowa ya kammala karatun boko ya rika tunanin sai gwamnati ta ba shi aikin yi. Za kuma a rage masu neman mukaman siyasa domin su azurta kawunansu.
Lallai lokaci ya yi da al’ummar Katsinawa za su duba kyawawan manufofin gwamnati su tallafa mata, domin taimakon kansu da kansu. Ita kuma gwamnati wajibi ne a kanta ta jawo duk wani ko wasu rukunin mutane masu kokari su zo a gudu tare, a tsira tare. Don ta haka ne kawai za mu kai ga nasara wajen shawo kan matsalolin al’umma.
Hassanu Baban Gado, Filin Samji Katsina.