Tsaro: Amurka ta turo jirage da sojoji zuwa Najeriya

Sojojin ba za su yi yaƙi kai-tsaye ba amma za su taimaka wajen tattara bayanan sirri.

Tsaro: Amurka ta turo jirage da sojoji zuwa Najeriya

Amurka ta tura jirage marasa matuƙa da sojoji 200 zuwa Najeriya domin taimakawa wajen yaƙi da matsalar tsaro.

Sai dai ƙasar ba ta tura sojojin domin yin faɗa kai-tsaye ba.

Aikinsu shi ne horaswa da kuma tattara bayanan sirri domin taimaka wa sojojin Najeriya.

Rahotanni sun ce an turo ne bayan Najeriya ta nemi taimako domin gano da kuma bibiyar barazanar ’yan ta’adda.

Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta tabbatar da cewa tawagar Amurka na aiki ne a wani filin jirgin sama a Jihar Bauchi.

Sun kuma ce ana amfani da jiragen ne wajen leƙen asiri kawai, ba kai hare-hare ba.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda ƙungiyoyi kamar Boko Haram da ISWAP ke ci gaba da kai hare-hare.

Jami’ai sun bayyana haɗin gwiwar a matsayin ƙoƙarin tunkarar barazanar tsaro da ƙasashen biyu ke fuskanta, tare da ƙarfafa musayar bayanan sirri.

Sun kuma ce tsawon lokacin aikin zai danganta ne da yarjejeniyar da ƙasashen biyu za su cimma, yayin da ake ƙara ƙarfafa ƙoƙarin yaƙi da ’yan ta’adda.