Tsaro: Gwamnatin Kaduna ta raba wa jami’an tsaro motoci 150 da babura 500
Gwamnatin ta jaddada ƙudurinta na bai wa sha’anin tsaro muhimmanci.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta sayi motoci 150 da babura 500 domin raba wa jami’an tsaro a jihar domin yaƙi da ‘yan bindiga.
Gwamnatin ta bayyana cewa, maƙasudin sayan kayayyakin shi ne tallafa wa jami’an tsaro a jihar don ci gaba da murƙushe ‘yan bindiga.
- Kotu ta hana ’yan sanda da sojoji fitar da Sanusi daga fada
- Harin Isra’ila Ya Tilasta Rufe Asibitin Gaza
A yayin ƙaddamar da motocin da babura mai taken “Operation Fushin Kada” Gwamnan Jihar, Sanata Uba Sani, ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare rayukan jama’a ta hanyar bayar da dukkanin tallafin da ya kamata ga hukumomin tsaro a jihar.
Ya kuma bayyana goyon bayan gwamnatinsa na samar da ‘yan sandan jihohi.
Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, a nasa jawabin, ya bayyana muhimmancin sintirin jami’an tsaro don daƙile yunƙurin mahara a jihar.
Ya kuma jaddada yadda gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen tabbatar da tsaro a faɗin jihar.
Kazalika, babban hafsan sojin ƙasa, Janar Christopher Musa, ya yaba da ƙwazo da ƙwarewar sojoji kan yadda suke fatattakar ‘yan bindiga a jihar.
Ya jaddada cewa ƙoƙarin da suke yi na samar da zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali a fadin ƙasar nan.
Ya yi nuni da cewa, motocin zirga-zirgar da aka bayar za su yi amfani da su yadda ya dace.
Janar Musa ya buƙace dakarun soji da su sake jajircewa wajen ganin sun kare martabar ƙasar nan da mutuncinta yayin da suke aiki da motocin.