Tsaro: Gwamnatin Yobe ta bai wa ’yan banga da mafarauta kyautar babura
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bai wa ’yan banga da mafarauta kyautar babura don kyautata harkar tsaro a jihar.
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bai wa ’yan banga da mafarauta kyautar babura don kyautata harkar tsaro a jihar.
Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkar tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya) ne, ya miƙa baburan ga ’yan bangar.
- ’Yan sanda sun kashe mutum 1, sun kama masu laifi 6 a Kaduna
- ’Yan sanda sun kama mutum 3 da jabun kuɗi N129bn a Kano
A lokacin, ya bayyana cewa wannan tallafin yana daga cikin ƙoƙarin gwamnatin na tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Abdulsalam, ya ce wannan ba shi ne karon farko da gwamnati ke tallafa wa ’yan banga da kayan aiki ba.
Ya ce ko a baya gwamnatin ta ba su irin wannan tallafi don su samu damar gudanar da ayyukansu cikin sauƙi da kwanciyar hankali.
Ya ce tsarin ya nuna ƙudirin gwamnatin na inganta tsaro da kuma tallafawa masu sa-kai don tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.