Tsaron Arewa: Tsakanin Gwamnoni da Shugaba Jonathan
A wata ziyara da gwamnonin Arewacin Najeriya suka kai kasar Amurka a watan Maris da ya gabata, gwamnonin sun tuhumi Shugaba Jonathan akan yanayin da tsaro ya tabarbare a kasar musamman a yankin Arewa maso Gabas, yadda yan kungiyar Boko Haram keta kashe jama’a da kone dokiyoyin su. A tasu mahangar, Shugaban kasa shi ke […]
A wata ziyara da gwamnonin Arewacin Najeriya suka kai kasar Amurka a watan Maris da ya gabata, gwamnonin sun tuhumi Shugaba Jonathan akan yanayin da tsaro ya tabarbare a kasar musamman a yankin Arewa maso Gabas, yadda yan kungiyar Boko Haram keta kashe jama’a da kone dokiyoyin su. A tasu mahangar, Shugaban kasa shi ke da Jami’an tsaro na soja da ‘yan sanda, amma ya ki tabuka wani abin azo agani don dakile matsalar, har ma suka tuhume shi da ya gaggauta bayyana wadanda ke ba ‘yanta’addan kudi da makamai.
Sai dai kuma, Shugaba Jonathan ya mayar da martani a yayin zuwan sa Bauchi a ranar 29/3/2014 don halartar wani taro da Jam’iyyar sa ta PDP ta shirya a yankin na Arewa maso Gabas, yadda ya shaida wa gwamnonin cewar, matsalolin da suke faruwan sun samo asali ne daga wurin su, sakamakon gazawar su wajen samar da ilimi wa jama’a da kuma rashin samar da ayyukan yi ga matasan yankin. Amma kuma shi (Shugaba Jonathan) a cewarsa, yana bakin kokarin sa don kawo karshen matsalar, duba ga irin sojoji da ‘yan sandan da ke jibge a yankin don shawo kan al’amarin.
Ga abin da Shugaba Jonathan ya fadi “ abun kunya ne ace gwamna yana kan karagar mulki na tsawon shekaru 6 ko sama da haka, amman yazo yana maganar rashin shugabanci nagari, bayan a jiharsa akwai matasa wadanda sama da rabin su ba su halarci makarantar firamare ba, kuma baya komai akai”
Shugaban ya kara da cewar “Gwamnonin Jihohi ne ya kamata su ji kunya idan yaranmu ba su halarci firamare da sakandare ba, kuma (yaran) suka dauki makamai (don yakar gwamnati)…. Ba aikin Shugaban ‘Yan sanda (IG of Police) ba ne ya rika tura yara firamare da sakandare ba, amma dokar tsarin mulkin Najeriya ta sanya Gwamnatin Tarayya ce ke da alhakin ganin yara (da suka gama sakandare) sun halarci makarantun gaba da sakandare…”
A wani rahoto da kungiyar kula da Ilimi da Al’adu ta Majalisar dinkin Duniya, wato UNESCO ta fitar a shekarar 2014, ya nuna cewar, akalla yaran da suka kai mizanin shiga makarantar firamare milyan 10.5 ne ke ta garari akan hanyoyi a Najeriya (ba su zuwa makaranta), wannan kuma daidai yake da cewar, yaro daya a cikin biyar bai zuwa makaranta ke nan a Najeriya. Wannan ya nuna cewar, kasar nan ce ta farko a cikin kasashe 12 da suka fi kowa wannan matsalar a duniya, domin ita ce ke da kashi 47 cikin 100 na yaran da ba su zuwa makaranta a duniya. Hakan kuma yana faruwa ne a kasar da ita ce ta takwas a cikin jerin kasashe masu tarin da albarkatun man fetur a duniya.
Idan muka dawo yadda matsalar ta tsaro tafi tsamari, wato Arewa maso Gabashin Najeriya, yankin da ya kunshi Jihohin Adamawa da Bauchi da Borno da Gombe da Taraba da Yobe, suna da jama’a akalla miliyan 19 (Kidaya, 2006). Wadannan Jihohin sun kashe kudade akalla tiriliyon 3.752 daga Shekarar 2005 zuwa 2013. Duk da cewar sama da 90 cikin 100na yaran da ba su zuwa makarantar daga yankin na Arewa suke, wadannan kudin kusan za mu iya cewar suna tafiya wasu wuraren da bai kamata su shiga ba, domin babu wani ci gaban da za a iya nunawa a yankin da ya kai wadannan makudan kudin musamman don ci gaban ilimin firamare da sakandare.
Kamar yadda Shugaba Jonathan ya fada, gwamnonin Jihohi suke da alhakin ba da ilimin firamare da sakandare a Jihohin su, wanda hakan ya gagaresu ya kuma sanya matasan da ba su je makaranta ba, daukar makamai don yakar gwamnatin da ta barsu cikin Jahilci da kuma Talauci. Idan da a ce gwamnonin sun kashe kashi 5 cikin 100 na wadannan kudin don bayar da ingantaccen ilimi kyauta a jihohin su, da zai yi wuya a samu wasu da za su dauki makamai don yakar gwamnati.
Marigayi Tsohon Shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela ya ce “ Ilimi shi ne babban makamin da za ka yi amfani da shi ka canza duniya” kuma ya kara da cewar “ Babu wata kasa da za ta ci gaba har sai ta ilmantar da ‘ya’yan ta.” Wannan shi zai nuna mana cewar, idan gwamnati ba za ta samar da ilimi wa ‘yan Najeriya ba, to batun ci gaba fa an barshi a baya, kuma wannan matsalar tsaron da ake fama da itan, ko da ta tafi, to za ta iya dawowa kamar yadda aka yi da matsalar Maitatsine a can baya, yau kuma sai ga Boko Haram ta dawo kuma akan akida daya. An kashe maciji an bar kansa.
Tunda ya kasance ku gwamnoni ne ke da alhakin samar da ilimin firamare dana sakandare a jihohin ku, to Shugaba Jonathan yana da gaskiya anan, kun gagara aiwatar da naku aikin kuma kuna tuhumarsa da cewar baya abin da ya kamanta, don samar da cikakken tsaro a yankunan ku, bayan irin makudan kudin da yake salwantarwa don kawo karshen al’amarin. Lallai Bahaushe ya yi gaskiya da ya ce ‘laifi tudu ne, hau naka ka hangi na wani’.
Sanin ku ne cewar, wannan irin tabarbarewar tsaron zai iya faruwane kuma yayi tasiri a yankin ku na arewa kawai don sakankancewar da kukayi akan bayar da ilimin firamare dana sakandare a yankin naku kyauta, domin kuwa gidajen watsa labarai sun sha rawaitowa irin sace sacen kudaden da ake warewa gina azujuwa, sayen littatafai da sauran abubuwan da za su ciyar da ilimin gaba a mafi yawan jihohin ku, amman mafi yawan lokuta, kukan yi shiru, domin dangantakar da ke tsakanin ku da wadanda suka yi rashin gaskiyar ko don wasu manufofi na siyasa.
Fatana a nan shine, ya kamata ku gwamnoni ku kara kwazo a wannan yanki naku, musamman ta hanyoyin samar da dokokin da suka danganci bayar da ilimin firamare da sakandare kyauta kuma na dole, kamar yadda Jihohin Legas da Kano suke yi a yanzu, don samar da ingantacciyar al’umma nan gaba. Matasan da lokacin su ya kure kuma, sai ku tallafe su da jari don yin sana’o’i, ku kuma karfafa aikin noma da kiwo don rage zaman banza wa jama’ar da suka zabe ku, da kuma yaki da cin hanci da rashawar da ya yi katutu a mafi yawan jihohinku, ta nuna ‘ba sani, ba sabo’ akan duk wanda zai saci kudin gwamnati.
Allah ya taimaki kasarmu Najeriya, amin.
Salisu Hassan Dango Yana, K/H Shira, Jihar Bauchi-Nigeriya [email protected], [email protected] +2348032875677.