Tsaron kasa ba na gwamnatin tarayya kadai ba ne -Yarima Oyakhire

Tsohon gwamnan jihohin Taraba da Oyo kuma mataimakin shugaban ’yan sandan Najeriya, mai murabus, Dokta Yarima Amon Oyakhire ya yi tsokaci a kan batun tabarbarewar tsaro da dorewar cin hanci da rashawa a kasar nan, inda ya shawarci ’yan siyasa da ke dafe da mukaman mulki, dangane da abin da ya shafi hakkin yi wa […]

Tsaron kasa ba na gwamnatin tarayya kadai ba ne -Yarima Oyakhire

Tsohon gwamnan jihohin Taraba da Oyo kuma mataimakin shugaban ’yan sandan Najeriya, mai murabus, Dokta Yarima Amon Oyakhire ya yi tsokaci a kan batun tabarbarewar tsaro da dorewar cin hanci da rashawa a kasar nan, inda ya shawarci ’yan siyasa da ke dafe da mukaman mulki, dangane da abin da ya shafi hakkin yi wa al’ummar kasa aiki cikin gaskiya da adalci.
Yarima Oyakhire ya yi tsokacin ne tare da ba da shawara a cikin wata hirarsu da wakilin Aminiya a garin Benin, inda kuma ya nuna batun raunin tsaro da yake ci gaba a kasar nan ruwan dare ne gama duniya.
“Lallai akwai matsalloli da dama tattare da batun tsaro a kasar nan, lamarin da ya kai matsayin jefa fargaba a zukatan al’umma, sai dai idan aka lura sosai, matsalar ba Najeriya kadai take fama da ita ba, a’a, har da sauran kasashen duniya baki daya, kodayake akwai ’yan bambance-bambance a tsakanin kasashen na duniya”. Inji shi.
Dokta Oyakhire ya ce duk da gwamnatin tarayya tana yawaita bayani a kan damuwarta na batun tsaro, wannan kadai ba zai iya magance komai ba, har sai al’ummar kasa sun tashi tsaye sun bayar da gudummawarsu ta fannin hadin kai da gwamnatin kafin komai ya tafi daidai.
Ya ce wannan lamari hakki ne da ya rataya ga wuyan kowane dan kasa, ba wai nauyin ita gwamnatin kadai ba,  “Domin in da tsaro, za a samu ci gaba da zaman lafiya a kasa, in kuwa aka rasa shi, dole jama’a za su shiga fargaba, har ta kai ga suna kaurace wa yankunan da suke domin tsirar da rayukansu” .
Dangane da batun cin hanci da rashawa da ke ci gaba da samun gindin zama a kasar nan kuwa, Yarima Oyakhire cewa ya yi, “Matukar ba an rabu da son zuciya ba, za a dade ana fama da matsalar cin hanci da rashawa, domin ba karamar illa take yi wa kasa ba, don haka sai an yi da gaske kafin a samu nasarar kawar da ita. Matsala ce da ta rigaya ta mamaye gwamnatocin kasashe duniya, ta fuskar siyasa da ta tattalin arzikin kasa da sauransu. A kasarmu Najeriya, matsala ce da ta yi wa ci gabanmu tarnaki, tana kara gurgunta sha’anin hakkokin jama’a, kuma tana rage kimar kasa a idon duniya. Ina ganin hanya daya tilo da gwamnati za ta bi domin rage yawan matsalar ita ce ta koma wa kyautata wa kowa da kowa, ta baiwa kowa hakkinsa na dan kasa, ba tare da nuna bambanci ba”.
A karshe, Dokta Oyakhire  ya shawarci ’yan siyasa da ke da mukamai tun daga gwamnatin tarayya har zuwa kananan hukumomi da su dubi lamarin da ya shafi rikon amana da cika alkawura. “Akasarin ’yan siyasar kasar nan ba su tunanin kyautata wa al’ummar da ta zabe su, alhali ita siyasa ana yin ta ne da manufar kawo ci gaban kasa da al’ummarta”.