Tsaron makarantu: An ƙaddamar da sabbin matakai a Gombe
’Yan sanda sun ƙaddamar da sabbin matakan ƙarfafa tsaro a makarantu bayan wani taron tattaunawa da Kwamishinan ’Yan Sanda da shugabannin Ƙungiyar Malaman Sakandare nq jihar Gombe
Daya daga cikin makarantun da ke garin Bunkure
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Gombe ta ƙaddamar da sabbin matakan ƙarfafa tsaro a makarantu bayan wata tattaunawa tsakanin Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Bello Yahaya, da Ƙungiyar Malaman Sakandare reshen jihar.
An gudanar da taron ne a Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Gombe, bisa umarnin Shugaban ’Yan Sanda na Ƙasa, Kayode Adeolu Egbetokun, na ƙara tsaurara tsaro a makarantu a faɗin ƙasar nan.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali kan duba tsarin tsaro na yanzu a makarantu, musamman waɗanda ke yankunan da ke da ƙalubale, tare da gano wuraren da ake buƙatar gaggawar gyara.
CP Bello Yahaya ya tabbatar da ƙudirin Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya na ci gaba da kare cibiyoyin ilimi, saboda dole bnebmakarantu su kasance wurare masu aminci domin koyo da koyarwa.
Ya jaddada muhimmancin yin nazarin tsaro a kai a kai, tsara matakan rigakafi, da kuma tabbatar da ci-gaba da haɗin gwiwa tsakanin shugabannin makarantu, Ma’aikatar Ilimi da hukumomin tsaro.
Kwamishinan ya bayyana cewa rundunar ta ƙara ƙarfafa sintiri, sa ido, da kuma gaggawar amsa kira a yankunan makarantu da aka fi ganin haɗarin tsaro.
Ya kuma bukaci shugabannin makarantu su riƙa kasancewa a shirin tuntuɓar ofisoshin ’yan sanda mafi kusa, tare da hanzarta ba da rahoton duk wani abin da ya haifar da zargi.
Ya yaba wa shugabannin ANCOPSS bisa jajircewarsu wajen aiki tare da hukumar ’yan sanda domin ƙarfafa tsaro a makarantu.
A nasu ɓangaren, shugabannin ANCOPSS sun gode wa rundunar ’yan sanda bisa ƙoƙarin da take yi na tabbatar da lafiyar dalibai da malamai, tare da alƙawarin yin aiki kafada da kafaɗa da rundunar da Ma’aikatar Ilimi domin ƙarfafa duk tsare-tsaren tsaro a makarantun sakandare.
Rundunar ta kuma yi kira ga iyaye, malamai, shugabannin al’umma, da mazauna unguwanni da su kasance masu lura da faɗakarwa, tare da tallafa wa duk wani yunƙurin inganta tsaro a makarantu, domin kiyaye rayuwar ɗalibai nauyi ne da ya rataya a kan kowa.