Tsawa ta halaka mai juna biyu a Kaduna
A makon jiya ne tsawa ta fada wa wata mata mai juna biyu mai suna Maryam Abdulkadir wanda ya yi sanadin rasuwarta a gidansu da ke Sanono, hayin Rigasa Kaduna.Shaidun gani da ido sun shaida wa Aminiya cewa al’marin ya faru ne da misalin karfe 7 na yamma, a lokacin da ake tsula ruwan sama […]
A makon jiya ne tsawa ta fada wa wata mata mai juna biyu mai suna Maryam Abdulkadir wanda ya yi sanadin rasuwarta a gidansu da ke Sanono, hayin Rigasa Kaduna.
Shaidun gani da ido sun shaida wa Aminiya cewa al’marin ya faru ne da misalin karfe 7 na yamma, a lokacin da ake tsula ruwan sama kamar da bakin kwarya.
An ce dai marigayiyar na zaune da ’yan uwanta a dakinsu ne lokacin da abin ya faru.
An ce ’yan uwanta na sa ran ta haihu a cikin watan nan da muke ciki amma Allah bai nufa hakan ba. “Tana da cikin wata takwas lokacin da abin ya faru. Duk mun sa rai za ta haihu a cikin watan nan na da muke ciki,” inji kakarta.
Rahotanni sun kuma nuna cewa wannan al’amari da ya faru ya matukar tada wa dukkan wadanda suka ga gawarta a kwance cikin daki, musamman ma mata hankali inda suka yi ta zubar da hawaye.
“Marigayiyar kalau take kafin a soma ruwan sama kamar da bakin kwarya. Muna zaune da ita a cikin daki sai ta ce da ni in tashi in dauko mata batir. Mikewa ta ke da wuya sai aka yi tsawa mai karfi daga nan sai walkiya ta biyo. Ina waigawa sai na ganta a kwance ta sandare. Ganin haka sai na yi sauri na debo ruwa na yayyafa mata ko za ta tashi amma ba ta tashi ba. Da na ga haka ne sai na fita cikin gida ina ihu, domin neman taimako.” Inji kanwarta Sadiya, cikin hawaye.
A cewar Sadiya, marigayiyar ba ta kone ba a sanadin walkiyar. “Da farko dai mun dauka ta kone a kafa amma da muka sake duba ta sai muka ga ba ta kone ba,” inji ta.
Ga dukkan alamu dai marigayiyar, wacce shekarunta ba su kasa 25 ba, ta rasu ne a sakamakon kila faduwar gaba ko kuma hucin tsawar da ta sauka a cikin gidan.