Tsawa ta hallaka shanu tara

Tsawa ta hallaka shanu tara yayin da wata karsana daya ta fadi ta kasa tashi bayan saukar wata tsawa a kusa da inda ake kiwata su a dajin Tudun Wadan Gidan Waya (Dajin Aden) da ke Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna. Lamarin, wanda ya faru da misalin karfe 10 zuwa 11 na dare a […]

Tsawa ta hallaka shanu tara

Tsawa ta hallaka shanu tara yayin da wata karsana daya ta fadi ta kasa tashi bayan saukar wata tsawa a kusa da inda ake kiwata su a dajin Tudun Wadan Gidan Waya (Dajin Aden) da ke Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna.

Lamarin, wanda ya faru da misalin karfe 10 zuwa 11 na dare a ranar Asabar da ta gabata ya biyo bayan tafka ruwan sama ne inda bayan saukar karar tsawar, sai shanun goma suka zube a kasa ba tare da ko kwarzanen ciwo a jikinsu ba,  kuma bayan zuwan Fulanin da ke kiwata su ne suka tarar da tara sun mutu daya kuma ta kasa tashi.

Lokacin da Aminiya ta isa dajin ta tarar da shanun tara da wadda ta kasa tashin.

Mai shanun Malam Ayuba Rabo, wanda aka fi sani da Baffate ya shaida wa Aminiya cewa shanun 10 su ne kusan abin da suka rage masa ga shi kuma tsawa ta hallaka su.

Malam Ayuba, ya ce abin da ya  faru ya san jarrabawa ce daga Allah, kuma ya ce babu abi nda zai ce face fatan Allah Ya maida masa abin da ya fi wannan alheri tare da fatan samun tallafi daga hukuma don ci gaba da sana’arsa ta kiwo.