Tsawa ta kashe mutum 6, ta jikkata 4 a Adamawa

Lamarin ya faru ne ranar Lahadi yayin da mamatan da waɗanda suka jikkata ke girbin gyaɗa ruwan sama kamar da bakin ƙwarya yana kwarara.

Tsawa ta kashe mutum 6, ta jikkata 4 a Adamawa

Tsawa

Mutum shida sun rasu, yayin da wasu huɗu suka jikkata bayan tsawa ta faɗa kansu a ƙauyen Dadiri-Tirgali da ke gundumar Garum a Ƙaramar Hukumar Ganye ta Jihar Adamawa.

Lamarin ya faru ne ranar Lahadi yayin da mamatan da waɗanda suka jikkata ke girbin gyaɗa ruwan sama kamar da bakin ƙwarya yana kwarara.

Shaidu sun ce huɗun da suka tsira suna karɓar magani a Babban Asibitin Ganye, yayin da al’ummar yankin suka shiga jimami sakamakon ibtila’in.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Ganye, Daniel Kamsobbi, da ya tabbatar da faruwar lamarin ya jajanta wa iyalan mamatan.

Ya ƙara da cewa an sallami wata uwa da ɗanta daga asibiti bayan an tabbatar da ƙoshin lafiyarsu, yayin da mutum biyu ke ci gaba da karɓar magani.

Ya ce an umarci ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro su binciki musabbabin lamarin domin taimakawa wajen wayar da kan al’umma, musamman manoma da ke yawan aiki a gonaki lokacin damina.

HOTUNA: An kama mutane 6 masu yi wa ’yan ta’adda safarar kayan masarufi a Borno

Shugaban Senegal ya zama sabon shugaban ECOWAS

Girgizar ƙasa ta yi ajalin mutum 6 a Peru

Mutum 6 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa