Tsawa ta kashe ’yan uwa 2 da dabobbi 144 a Sakkwato
Ruwan sama da tsawar sun yi sanadin rushewar gidaje da dama.
Wasu kananan yara ’yan uwan juna sun gamu da ajalinsu yayin da tsawa ta fada musu a kauyen Ja’oje a Karamar Hukumar Wamakko ta Jihar Sakkwato.
Kananan yaran masu shekara tara da kuma 11 masu suna Hamida da Maryam sun gamu da ajalin nasu ne a lokacin da suke barci a yayin da tsawar ta kayar da dakin da suke ciki.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Daraktan Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar, Mustapha Umar, ya ce dabobbi 144 sun mutu a sanadiyyar tsawar.
Ya ce tsawar ta fado ne a sakamakon mamakon ruwan sama da aka tafka a ranar Alhamis ta kuma rusa gidajen mutum sama da 177.
A cewar jami’in, hukumar da wasu kungiyoyi masu zaman kansu a jihar sun ziyarci kauyen don gudanar da bincike kan irin barnar da tsawar ta yi.
Ya tabbatar da cewa mutum biyu ne suka rasa rayukansu a iftila’in, amma ana ci gaba da bincike don gano ko akwai karin wasu da abun ya shafa.