Tsawon gemu ya sa dan Pakistan ya rasa aikinsa a Dubai

Gemu ya hana wani mutumin kasarPakistan samun aiki a Dubai da ke cikin Hadaddiyar Daular Larabawa. Mutumin dan shekara 21, mai sunan Jehangir Khan, ya samu aikin da za a rika biyansa kimanin Dirhami dubu da 300 (Naira Dubu 52 a kowane wata, kuma kudin sun nunka abin da yake samu wajen aikin burodi har […]

Tsawon gemu ya sa dan Pakistan ya rasa aikinsa a Dubai
Tsawon gemu ya sa dan Pakistan ya rasa aikinsa a Dubai

Gemu ya hana wani mutumin kasarPakistan samun aiki a Dubai da ke cikin Hadaddiyar Daular Larabawa. Mutumin dan shekara 21, mai sunan Jehangir Khan, ya samu aikin da za a rika biyansa kimanin Dirhami dubu da 300 (Naira Dubu 52 a kowane wata, kuma kudin sun nunka abin da yake samu wajen aikin burodi har sau hudu a kasarsa ta haihuwa.

Jehangir Khan, wanda ya fito daga gundumar swabi da ke Khyber Pakhtunkhwa, ya ce an hana shi aikin dakin girki ne a wani gidan abincin mutanen Italiya, bayan da ya ki aske gemunsa, kamar yadda gidan sayar da abincin ya bukace shi da ya yi.
“Sun kawo Dubai, inda suka samar mini da bisar izinin yin aiki a Agustan da ya wuce, amma da aka zo ba ni izinin zama a kasar, sai suka ki amincewa, wai saboda na ki askewa ko rage gemuna,” a cewarsa, cikin hirar da ya yi da kafar yada labarai ta dPRESS.
Khan ya ce bai taba aske gemunsa ba, a tsawon rayuwarsa, amma a shirye yake ya dan dates shi. Sai dai wadanda sukadauke shi aiki suna son ya kwalkwale komai,ya share gashin gemun gaba daya. “A gaskiya ban shirya yin haka ba, a tsawon rayuwata, ko ma me zai faru duk da cewa na rasa aikina, amma dai abin da nike bukatar wannan kamfani ya yi mini shi ne, su biya ni kudin duk da na kashe.