Tseren Babura: Gasar farko bayan COVID-19 ta samu matsala

Miguel Oliveira, direben kungiyar Red Bull ya lashe Gasar Tseren Babura na MotoGP Thailand Grand Prix ranar Lahadi 2 ga Oktoba, 2022.

Tseren Babura: Gasar farko bayan COVID-19 ta samu matsala

Miguel Oliveira, direben kamfanin Red Bull KTM yana muna bayan lashe Gasar Tseren Babura na MotoGP Thailand Grand Prix ranar Lahadi 2 ga Oktoba, 2022. (Hoto: Manan VATSYAYANA/AFP)

Miguel Oliveira, direben kungiyar Red Bull dan kasar Portugal ya lashe Gasar Tseren Babura na MotoGP Thailand Grand Prix ranar Lahadi 2 ga Oktoba, 2022.

Gasar wadda ita ce ta ta farko cikin shekara uku kasar Thailan ta samu tsaiko sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a filin tsere na Buriram Circuit.

Ruwan ya sa dole aka dakatar da wannan wasan tseren babura da aka shirya farawa karfe 8:00 na safe agogon GMT da minti 55.

Rabon da a gudanar da gasar a kasar tun a shekarar 2019, da aka samu bullar cutar COVID-19, wadda ta kawo tsaiko ga harkoki da dama ciki har da wasanni a fadin duniya.

Baya an samu hasashen yiwuwar samun ruwan sama tun daga ranar Juma’a, amma ba a samu ruwan ba sai ranar Lahadi da aka shirya fara gasar, wanda ya kawo tsaikon da wasan Moto2 da aka shirya.

An shirya wasan zai fara ne da Marco Bezzecchi na kasar Italiya a sahul farko na MotoGP tare da Jorge Martin na kasar Spain da kuma Francesco Bagnaia.

Rabon kasar da gudanar da gasar MotoGP tun shekarar 2019 da aka samu bullar cutar COVID-19.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50