Tsigau a Nasarawa: ’Yan majalisa sun koma da zama a yankin Karu

’Yan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa sun gudu daga Lafiya babban birnin jihar inda suka koma da zama a yankin karamar Hukumar Karu da ke kusa da Abuja a kokarin da suke yi na tsige Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura.’Yan majalisar sun zauna a Karu ne a shekaranjiya Laraba, inda suka tattauna kan korafin da aka […]

Tsigau a Nasarawa: ’Yan majalisa sun koma da zama a yankin Karu
Tsigau a Nasarawa: ’Yan majalisa sun koma da zama a yankin Karu

’Yan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa sun gudu daga Lafiya babban birnin jihar inda suka koma da zama a yankin karamar Hukumar Karu da ke kusa da Abuja a kokarin da suke yi na tsige Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura.
’Yan majalisar sun zauna a Karu ne a shekaranjiya Laraba, inda suka tattauna kan korafin da aka rubuta game da yadda Babban Jojin Jihar Mai shari’a Suleiman Dikko ya nada wakilan kwamitin mutum bakwai da za su binciki zarge-zargen da suke yi wa Gwamna Al-Makura, inda suka bukaci ya canja wasu wakilan kwamitin da suka ce ba su gamsu su kasance wakilan kwamitin ba.
Majalisar mai rinjayen ‘’ya’yan Jam’iyyar PDP ta bukaci Babban Jojin ne ya kafa kwamitin a wani bangare na yunkurin tsige Gwamnan. Kuma Jam’iyyar APC ta Gwamna Al-Makura ta musanta cewa Gwamnan ya aikata ba daidai ba, inda ta la’anci yunkurin tsige shi tare da zargin PDP da Fadar Shugaban kasa da iza wutar tsigau din.
Babu wani bayani kan dalilin da ya sa ’yan majalisar suka kaurace wa ginin majalisar da ke Lafiya suka koma Karu da ke kusa da Abuja da zama.
Sai dai ana fama da zanga-zangar nuna rashin amincewa da yunkurin tsige Gwamna a dukkan sassan jihar.