Tsige Al-Makura: Za a yi hayar tsohon Babban Jojin Najeriya

Mai yiwuwa wani tsohon Babban Jojin Najeriya ya amshi aikin Babban Jojin Jihar Nasarawa Mai shari’a Sulaiman Dikko don taimakawa wajen aiwatar da shirin tsige Gwamna Umaru Tanko Al-Makura.A shekaranjiya Laraba ce Majalisar Dokokin Jihar ta amince da wani kudiri da ke umartar Babban Jojin Jihar ya kafa kwamitin bincike kan zarge-zarge 16 da ke […]

Tsige Al-Makura: Za a yi hayar tsohon Babban Jojin Najeriya
Tsige Al-Makura: Za a yi hayar tsohon Babban Jojin Najeriya

Mai yiwuwa wani tsohon Babban Jojin Najeriya ya amshi aikin Babban Jojin Jihar Nasarawa Mai shari’a Sulaiman Dikko don taimakawa wajen aiwatar da shirin tsige Gwamna Umaru Tanko Al-Makura.
A shekaranjiya Laraba ce Majalisar Dokokin Jihar ta amince da wani kudiri da ke umartar Babban Jojin Jihar ya kafa kwamitin bincike kan zarge-zarge 16 da ke cikin sanarwar tsige Gwamnan da ’yan majalisar suka sanya wa hannu.
Aminiya ta samu bayanin cewa, wasu suna tsoron ba za a samu nasarar tsige Gwamnan ba a hannun Babban Jojin Jihar, domin reshe zai juye da mujiya saboda wasu kura-kurai da suka shafi tsarin mulki kan yadda aka shirya tsigewar, ciki har da hanyar da majalisar ta aike da sanarawar.
Kuma sanin cewa Mai shari’a Dikko mutum ne mai tsananin bin ka’idar doka da ba zai lamunci son kai ba, sai aka yanke shawarar hayo wani a madadinsa.
Wata majiya ta yi zargin cewa hayo madadin ya janyo aka zabo wani tsohon Babban Jojin Najeriya daga wata jiha ta Arewa ta Tsakiya domin a tausasa Mai shari’a Dikko tare da sanya shi ya tankwara ka’ida domin karfafa yadda za a tsige Gwamnan.
Har zuwa hada wannan rahoto babu wani bayani kan ko majalisar ta sanar da Babban Jojin Jihar kan ya ci gaba da kafa kwamitin, yayin da Akawun Majalisar Mista Ego Maikeffi ya ki amsa kiran waya da aka ta yi masa don jin albarkacin bakinsa kan lamarin.
A wani labarin, Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ce al’ummar jihar za su tubure wa duk wani yunkuri da ’yan majalisar jihar za su yi don tsige Gwamna Umaru Tanko Al-Makura ta haramtacciyar hanya da nuna karfi.
Kakakin Gwamnan, Abdulhamid Kwarra ya shaida wa manema labarai a shekaranjiya Laraba cewa: “Dagewar da majalisar ta yi ta keta tsarin mulki da karya doka domin cire Gwamnan da karfin cin tuwo zai hadu da turjiya daga al’ummar Jihar Nasarawa.”
Kwarra yana magana ne kan zaman majalisar da ya umarci Babban Jojin Jihar ya kafa kwamitin mutum bakwai don bincikar zarge-zarge 16 da ke cikin takardar sanarwar tsigewar da suka amince da ita a ranar 14 ga Yuli.
Ya ce gwamnatin jihar ta yi imani kuma tana tsare doka da oda da bin ka’ida, amma ya nanata cewa gwamnatin za ta amsa zarge-zargen ne kawai idan ’yan majalisar suka bi ka’idojin tsarin mulki, inda ya ce abubuwan da majalisar ke yi a mako gudan nan ya saba wa tsarin mulkin 1999.
Ya ce, matsayin gwamnatin shi ne har zuwa ranar Laraba majalisar ba ta aika wa Gwamnan da sanarwar tsigerwa ba, kamar yadda doka ta nema, kuma ya ce buga sanarwar a jaridu bai isa ba, domin kotu ce kawai ke iya bayar da wannan dama. “Bai dace majalisar ta ba kanta ikon zama alkali ba,” inji Kwarra.
Gwamna Al-Makura ya koma Lafiya a yammacin Talata bayan shafe mako guda shi da wasu mukarrabansa a Abuja, sai dai Aminiya ta lura ya shiga birnin ne ba tare da jiniya kamar yadda aka saba ba, kuma ya ci gaba da yin taro da mukarrabansa. Abu ne mai wahala a ce ga inda Gwaman yake saboda wata majiya ta ce ba ya gidan gwamnati.