Tsige Sarkin Musulmi: Ka rika bincike kafin yin magana —Gwamnan Sakkwato ga Shettima

Gwamnatin jihar ta ce ya kamata Shettima ya rika bincike ya tabbatar da gaskiya al’amari kafin ya yi tsokaci a kai.

Tsige Sarkin Musulmi: Ka rika bincike kafin yin magana —Gwamnan Sakkwato ga Shettima

Gwamnatin Sakkwato ta yi martani ga Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima kan kalamansa game da zargin gwamnan jihar da neman tsige Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar.

Gwamnatin jihar ta ce ya kamata Shettima ya rika bincike ya tabbatar da gaskiya al’amari kafin ya yi tsokaci a kai.

Raddin na zuwa ne bayan gargadin da Shettima ya yi wa gwamnatin jihar cewa ta yi hatara da kujerar Sarkin Musulmi saboda muhimmacin matsayin basaraken abu ne da ya kamata duk Najeriya  ta mutunta, ta girmama ta kuma kare ta.

Mataimkain shugaban kasar ya yi gargadin ne a taron tsaro da zaman lafiya na yankin Arewa maso yamma ranar Litinin a Jihar Katsina inda mataimakin gwamnan Sakkwato ya wakilci Gwamna Ahmad Aliyu.

Aminiya ta ruwaito Kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC) na zargin Gwamna Ahmad Aliyu da neman tsige Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci a Najeriya, kamar yadda gwamnan ya sauke wasu sarakunan gargaji 15 a kwanakin baya.

A martanin Gwamna Ahmad Aliyu ga Shettimma, ya bukaci mataimakin shuganan kasar ya rika bari sai ya san hakikanin gaskiyar al’amari, musamman wanda ya shafi kasa, kafin ya yi magana a kai.

A cikin sanarwar da kakakin gwamnan, Abubakar Bawa, ya sa wa hannu, ya ce, “Mun dauka mataimakin shguaban kasa zai yi hikimar tuntubar gwamna kafin ya yi magana kan lamarin a cikin jama’a.

“A matsayinsa na dattijo kuma uban kasa, ya kamata ya bari sai ya samu hujjoji kafin ya yanke hukunci a kan al’amarin da masu neman hana ruwa gudu ke shiryawa musamman a kafofin sada zumunta.

“Gaskiyar lamari ita ce ba mu awa wani shirin tsige Sarkin Musulumi kuma babu barazanar da muka yi masa.

“Sarkin Musulmi na da cikakken iko da ya dace da ofishinsa kuma ba mu taba tauye masa hakki ba.

“Saboda haka maganar a ce mu ba shi kariya da girmamawa ba ta ma taso ba, domin wannan aikimu ne.

“Gwamnati da al’ummar Sakkwato na goyon baya tare da girmma Sarkin Musulmi kuma muna tabbatar wa al’umma cewa za mu ci gaba da yin duk abin da ya dace domin kare Fadar Sarkin Musulmi a kowane lokaci,” in ji sanarwar.

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya