Tsintsiya ta koma lema?

Ba wani abu ya sa na sako waiwayo wannan batu na Tsintsiya da Lema ba sai ganin abin da ya faru kwanan nan a lokacin da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP a jihar Adamawa karkashin jagorancin Ahmed Gulak, tsohon mai bai wa tson Shugaba Jonathan Shawara suka yi wankan tsarki suka tsunduma cikin jam’iyyar APC, bisa […]

Tsintsiya ta koma lema?

Ba wani abu ya sa na sako waiwayo wannan batu na Tsintsiya da Lema ba sai ganin abin da ya faru kwanan nan a lokacin da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP a jihar Adamawa karkashin jagorancin Ahmed Gulak, tsohon mai bai wa tson Shugaba Jonathan Shawara suka yi wankan tsarki suka tsunduma cikin jam’iyyar APC, bisa kokarinsu na binne jam’iyyar PDP a jihar. Batun da ya ja hankalina shi ne jawabin da Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC a Arewa maso Gabas, Alhaji Mustafa Salihu ya yi don karbar bakin nasu, ya ce: “Ai ku ‘yan uwan tagwaicinmu ne, abin da ya faru shi ne mun riga ku barin jam’iyyar PDP ne zuwa APC, ku sai yanzu kuka gano bakin zaren. Kun fahimci tsiyar da jam’iyyar PDP ta tafka a kasar nan a baya, yanzu kun gane gaskiya, kun dawo jam’iyyar APC, muna maraba da ku.”

Wannan abu ni bai sa na yi mamaki ba, sai ma ya kara tabbatar mani da abin da na dade da sani ne, cewa hada-hadar siyasa irin ta Nijeriya ba ta gaji tunani da natsuwa da auna batutuwa ba. Abin da aka sani shi ne inda za a samu na cin abinci, ba batun akida ko neman shiga inda za a yi wa al’umma aiki, fakat.

Na san wasu za su ce, ai ita da ma siyasa irin ta Nijeriya haka ta gada; kwamacala, rashin kan gado, barna da lalaci da lalatawa. Wasu ma iya cewa ai rashin madafa shi ne siyasar Nijeriya ko kuma munafinci da almundahana da rashin sanin makoma. Amma a duk lokacin da mutum ya natsu, ya yi nazari, ya kuma fuskanci yadda wasu al’ummomi a wadansu kasashe ke gudanar da siyasar da yadda can kwamacalar da kwadon siyasa mai ciwowa ne, ba na yadawa ba, sai ya kara natsuwa cikin aminci da cewa, kila dai siyasar Nijeriyar ce da wasu irin ta, ba su da kan gadon. kila ‘yan siyasar Nijeriya ne ba su san yadda ake zuba tuwon siyasa, kabaki-kabaki a cikin kwarya ba. kila kasar Nijeriya ce ba ta iya shuka iri a tata gonar siyasar ba ko kuma ba ta da irin na kwarai, kamar yadda ake shuka shi a wadansu kasashe, ba tare da an sa masa takin zamani ba!

Me ya sa na tabbatar da haka? Abin da ya faru a Adamawa kwanan nan da kuma irin sa da ya faru ko yake ta faruwa a wasu sassan kasar nan ya yi nuni da haka. A halin yanzu idan muka ce nan da 2019 ba abin mamaki ba ne in muka kasance cikin tsarin jam’iyya daya, wato ta Tsintsiya ba zai zama da mamaki ba, musamman ganin yadda jam’iyyar nan mai Lema ta shiga cikin rudu da neman wargajewa, sa’annan kuma wasu na ta murna cewa ai gara Shegiyar Uwa ta mutu, a share ta da Tsintsiya. Wane irin tunani ne wannan? Alhali kuma mun sani cewa a duk lokacin da ake sharewa da kwashewa sai ka ga ana sake zuba dattin a cikin dakuna ko falon jam’iyyar Tsintsiya. Ni kuwa a nawa tunanin, kai ko yaro dan shekara takwas ka tambaya zai bayyana maka cewa, duk inda aka yi amfani da Tsintsiya aka yi shara, dattin nan da aka share a cikin kwandon shara ko bola ake zuba shi, ba wai a kai shi cikin uwar daki ba, ana yi masa goma sha tara ta arziki, kamar yadda muke gani a halin yanzu yadda ake tururuwa zuwa jam’iyyar Tsintsiya ana barin Lemar da aka ce kazanta ce tun farko! Ko dai Tsintsiyar ta koma Lemar ne ba a sani ba?

Domin fahimtar amsar wannan tambaya da kyau sai an koma ga tushe, mu tambayi kanmu to wai mene ne asasi? Me ya jawo wannan tabargaza a siyasarmu? Me ya sa mu kullum muke shiga cikin daki ido rufe? Me ya sa za a sharo dattin dakin lalatattar Lema  a kuma nemi sabon dakin Tsintsiya, a sake zuba dattin a cikin? Zan dawo kan wannan batun nan gaba!

Domin mu fahimci inda aka fito bari mu koma baya cikin tarihi, mu ga shin haka ake yi a wasu sassa na duniya dangane da siyasa da tsarin dimokuradiyya ko kuwa dai mu ne muke wa kanmu wuji-wuji gano gabas, amma mu kare muna kallon sama a matsayin gabas din?

Bari na soma da misalai guda biyu kawai na yadda siyasa da tsarin dimokuradiyya ke wakana a wasu kasashe, ciki har da wadanda muka ko muke kwaikwayo a tamu tafiyar. kila bisa wannan fasali mu amince tamu siyasar, ba siyasa ba ce, sayayya ce da rana kiri-kiri.

Tsarin siyasa da gudanar da al’amurran dimokuradiyya a ko’ina ya samu tsayuwa da gudanawa, abubuwa biyu ne suka assasa da tabbatar da shi. Na farko tsarin jam’iyya da mutanen da ke shiga cikin jam’iyyar. Na biyu kuwa fasalce-fasalcen tsarin shugabancin jami’iyyar da tsaren-tsaren da ta gindaya don ciyar da kasa da kuma al’umma gaba. Shi ya sa a wasu sassa na duniya za a tarar da jam’iyya daya ce ke godon mulki, ita kuma din da tsare-tsarenta da manufofinta da kuma hanyoyin aiwatar da su. Wata sa’a saboda dila rashin gudanar da al’amurra yadda ya dace ko kuma saboda gajiya da tsohon tsarin da wannan jam’iya take gabatarwa yake yi, sai a ga an samu jam’iyya mai adawa da wannan da ta yi dattin hula, ko kuma a samu wata da sauran jama’ar kasa ke ganin tsari da manufofinta sun fi wanda aka dade ana damawa da ita. Ta haka ne ake samun jam’iyya biyu ko uku suna tashe a cikin kasa domin a samar da zabi ga wadanda suka gaji da lamin wata siyasa.

Idan muka yi la’akari da irin wannan tsari sai mu ga cewa, ke nan idan an ga hayayyafar jam’iyyun siyasa a cikin tsarin gudanar da dimokuradiyya to ba wai alamun ci gaba ba ne, ni a tawa fahimta, alamun rarrabuwa ce da sukurkucewa da lalacewa. Wani na iya cewa amma ai tsarin dimokuradiyya ne ya bayar da wannan dama, domin tsari ne na gwamnatin jama’a don samar da ribar dimokuradiyya ga jama’ar. Amma idan muka natsu sosai za mu ga cewa kasashe kamar su Amurka da Rasha da Ingila da sauran irin su, ai suna sane da wannan tunanin, amma suka takaita ko suka kasance sun zaba wa al’ummar su jam’iyyu biyu, manya, masu gudanar da mulki domin jama’arsu. Duk da haka ba su bari komi ya tabarbare ko zuguguce ba.

Za Mu Ci Gaba