Tsintsiya ta koma lema (2)

A tuna, irin wadannan al’umma ba zama suka yi suka ce lallai ilau jam’iyyu biyu za su kasance a cikin kasar ba, a’a, suna dai da tabbatacin cewa ai dan Adam fuska biyu ce gare shi, ko dai mai ra’ayin rikau ko mai son kawo sauyi, ko da kuwa a cikin tsari na kwaminisanci ne […]

Tsintsiya ta koma lema (2)
Tsintsiya ta koma lema (2)

A tuna, irin wadannan al’umma ba zama suka yi suka ce lallai ilau jam’iyyu biyu za su kasance a cikin kasar ba, a’a, suna dai da tabbatacin cewa ai dan Adam fuska biyu ce gare shi, ko dai mai ra’ayin rikau ko mai son kawo sauyi, ko da kuwa a cikin tsari na kwaminisanci ne ko na jari hujja. Ko da kuma a cikin tsari ne na gargajiya ko na sarauta ko kuma na gado, haka abin yake. Haka kuma ko da a cikin tsari ne na addini, sai an samu irin wannan rarrabuwa. Saboda haka, biyu ta fi daya, ta kuma fi uku ko barkatai, in dai gaskiya ake bukata.  

Ke nan ana iya cewa Amurkawa ko Rashawa ko Biritaniyawa ko Larabawa ko Asiyawa da makantan su, sun yi haka, ni a tawa fahimta saboda sun yi amanna cewa dan Adam yana iya kasancewa wanda ake dannewa ko wanda ke dannewa! In abubuwa sun yi kamari ne ake samun ‘yan tsaka-tsaki ko ‘yan ba-ruwanmu, wadanda su ba su amince da daya daga cikin wadannnan tsare-tsare ba.

Shi ya sa a Amurka tsarin siyasarta da dimokuradiyyarta ya kasance jam’iyyu biyu ne manya, a cikin tsarin jari-hujja, su ne kuma ake ta fafatawa da su cikin tsawon shekara 200. Ko dai jam’iyyar Democrats ko kuma Rebuplicans. A kuma kula, ba wai haka nan wadannan jam’iyyu suka wanzu da karfin gwamnati ba, ‘a’a, tsari ne na gudanuwar al’umma a tsawon lokaci.

Abin la’akari da tsarin jam’iyyun da ake da su a wasu sassa na duniya da kuma dangantakar su da al’ummar da ke cikin su, ba irin ta auren zobe ba ce, ga wasu, auren mutu ka raba ne. Ba wani abu ya sa na fadi haka ba sai ganin wadanda ke cikin wadannan jam’iyyun sun yi amanna da tsare-tsare da manufofi da sauran lamurran gudanar da siyasa, suna kuma tokabo da su. 

Ko da kuwa a cikin babban tsari na kasa da akidojin gudanar da mulki a cikin kasar duk siffa guda ke gare su. Misali, ‘yan Democrats na Amurka ba masu bin gurguzu ko kwaminasanci ba ne, a’a, ‘yan tsaka-tsaki ne, abin da suke kire da liberals. Duk da cewa babbar manufar kasar da tsarin gudanar da ita saiti daya gare shi, wato tsarin jari hujja, wanda shi ne akidar tattalin arzikin da gudanar da lamurran kasa, amma sun amince da akwai masu rauni don haka ya dace a samar da mafi karancin albashi ga al’umma, sa’annan kuma a maka wa masu tarin dukiya harajin gani da fada. 

Wannan kuwa ya yi hannun riga da daya jam’iyyar siyasar wato ta ‘yan Republicans, wadanda suke ganin tsarin tattalin arzikin kasa kamata ya yi ya bar kowa ya ji a jikinsa, ke nan bai dace ba a tsara wani abu wai shi mafi karancin albashi, sa’annan ba su amince da zabga haraji ga mai karfi ko mara karfi ba, domin a nasu tunanin dukiya jarin mai ita ce.

Wadannan akidu ne da ‘yan wadannan jam’iyyun siyasa suka amince da su, da su ake gudanar da rayuwa, ba ciri ba coge, sai inda ba a rasa ba. Shi ya sa alamun jam’iyyun ma suke dauke da wannan tunani. JAKI, shi ne alamar ‘yan Democrats, alhali GIWA ce alama ga ‘yan Republicans. A duk lokacin da ka ga ana yakin neman zabe a Amurka bisa wannan tunani ake yi, duk kuwa da dodoridon tsarin kasa da ke boye da kowannen ya amince da shi.

Haka wannan batu yake a Biritaniya ko Ingila, jam’iyyu biyu ne suke amayar da amonsu, ko dai Labour ko kuma Conserbatibes. ‘Yan Labour su ne masu tattare da ‘talakawa’ su kuwa Conserbatibes, masu ‘ra’ayin rikau’ ne, ‘yan mazan jiya, wadanda ba su yarda da rarraba dukiya ko tattalar ta domin wasu gungun al’umma ba, a bar kowa ya yi kurme cikin tekun tattalin arziki, kuma iya ruwa, fidda-kai ne a tunaninsu, wanda ya sha bamban da na ‘yan Labour. In da ake samun dan canji shi ne, a Ingila akwai Liberals, wadanda su kuma ba sa bin hagun baki daya, sa’annan ba sa zaune daram a damar, a cikin tsarin siyasar ta jari hujja.

Mun dauki wannan dogon lokaci muna wannan bayani saboda a fahimci cewa komi da tsari ya fi armashi ko da kuwa cikin babban tsarin na kasa ana samun lauje a cikin nadi. A kasashe kamar Amurka da Ingila, a tsawon shekaru, jama’a sun kama turba guda, cikin wannan turba suke tafiya, ‘ya’ya da jikoki, wasu har zuwa ga tattaba-kunne. Muhimmancin irin wannan tsari yana da dangantaka ne da dora kasa bisa alkiblar da ta dace, ba wai kallon mutane da ke cikin jam’iyyun ba ko wadanda ke shugabancin jam’iyyar siyasa ba. Manufa ita ce abin kula, ba wai jam’iyyar siyasar ba. 

Za Mu Ci Gaba…