Tsintsiya ta koma lema (3)
Idan muka auna ko kwatanta wannan da abin da ke faruwa a cikin kasar nan, za mu ga cewa tsarin namu a shiririce yake, inda ma ake da shi ke nan. Wata sa’a kuma kana iya cewa ba tsarin balle a yi godo da shi. Yanzu duk wanda ka tambaya mene ne tsari ko manufar […]
Idan muka auna ko kwatanta wannan da abin da ke faruwa a cikin kasar nan, za mu ga cewa tsarin namu a shiririce yake, inda ma ake da shi ke nan. Wata sa’a kuma kana iya cewa ba tsarin balle a yi godo da shi. Yanzu duk wanda ka tambaya mene ne tsari ko manufar jam’iyyar Tsintsiya ko kuma jam’iyyar Lema da ta dade tana mulki a kasar da wuya ka samu mai iya tabbatar maka da su. Idan ka ce ai jam’iyyar Lema ce kadai ta kasance mai fuska daya daga cikin sauran jam’iyyun da ake da su (idan ban da kila jam’iyyar Makulli ta Balarabe Musa) ba za a ce ka shara ta ba, shi ma ba wani abu ya jawo haka ba sai ganin don sun kasance bisa gadon mulki na tsawon shekara 16, kuma da yake lagwadar siyasa da dimokuradiyya suna tattare da mulki ko dai a matakin karamar hukuma ko jiha ko Gwamnatin Tarayya, musamman a Najeriya, da wuya irin wannan jam’iyya ta canja salo cikin kankanen lokaci.
Amma ita kanta jam’iyyar Tsintsiyar da aka samar a shekarar 2013, ta hau mulki a shekarar 2015, idan ka hankada labulen dakin nata abubuwa da za ka iske a cikin dakin, suna da yawan gaske. Nan ne aka samar da hadakar ACN, wadda kafin nan ita ce ake ce da AC, sa’annan ta taba zama AD (ita kuma AD ai hadaka ce tsakanin jam’iyyar Justice da ACD da wasu da dama) tun daga 2006. A cikin Tsintsiyar kuma yau akwai Jam’iyyar CPC, gyauron wasu jam’iyyun na baya. Akwai ANPP da APGA, dukkansu gyauro ne na wasu jam’iyyun ko kuma wasu ’yan gudun hijirar da suka baro wasu jam’iyyun da a da ba su ji dadin zama ciki ba. Irin wannan hadaka ta mabambantan ra’ayoyi da manufofi da akidoji da yawa ita ce ta kasance Tsintsiya, daurarra, ko ba komai hannayen da za su kama domin yin sharar suna da yawa, sa’annan ga kowane da irin datti ko sharar da yake fatar ya kai gare ta. Jayayya a irin wannan hali, abu ne da ba za a rasa ba, ana so ko ba a so.
To amma ni ba wannan ne ya fi damuna ba, ina kallon batun ne ta fuskar yadda Najeriya za ta karu da wannan haduwa ta Tsintsiya idan har ta fice daga yagaggar Lema. Me ya sa na ce haka? Ba abin dulmiya tunani irin yadda sharar da Tsintsiya ke yi ke neman komawa irin tsayuwar mai shika, tana fuskantar inda iska ke bugawa, a maimakon ta ba bugun iskar baya, ta yadda kaikayin ke komawa jikin mai shikar.
Don Allah ina amfanin gwamnatin Tsintsiyar da ke tafe da sharar dakin Lema da karikitanta, kila ma ana ji, ana gani mai doki yana komawa kan kuturi tun daga mazaba har zuwa fadar ASO. Wannan tsari shi ne ci gaba, ko shi ne mafita?
Wani abu da na tabbata jama’ar Najeriya ke bukata a halin da ake ciki yanzu shi ne canji, sai da alama shugabannin da ke dauke da tarin Tsintsiya a yanzu, canjin da kila suke neman su kawo wa kasar shi ne na ajiye Lema a dauki Tsintsiya a makwafinta. A lura duk irin shan rana da dukan ruwan saman da ’yan Najeriya suka yi ta fama da su tun daga 1999 zuwa yau, ba shi ne abin damuwa ba. Idan shugabannin Lema za su sake sheka, su kasance kansiloli da ciyamomi da gwamnoni da ’yan Majalisar Tarayya da Shugaban kasa da sauran mukarraban gwamnati dauke da tulin Tsintsiya a hannunsu, su a ganinsu, wannan shi ne canji. Idan kuma an natsu an yi nazarin abin da ke faruwa a halin yanzu za a ga alamun haka. Mene ne hujja?
Bari mu soma da wasu misalai na fili kafin mu leka na boye. A Jihar Kaduna, wadansu daga cikin tsofaffin shugabannin Lema da suka sake sheka zuwa Tsintsiya, an yi taron karbarsu, wadansu kuma daga cikin tsofaffin shugabannin har bude baki suka yi suna fada wa ’yan Tsintsiyar da suka tarbe su da su yafe musu laifin da suka yi musu a can baya. Wani da ya mike cewa ya yi, lallai mun san cewa a zaben da ya wuce mun cuce ku, mun hana ku ci zabe, mun sace akwatunan zabe, mun yi zurmuken kuri’u, domin mu tabbata Lema ta ci zabe, a yafe mana wannan laifi. Har nuna wani ya yi a cikin masu canja shekar cewa shi ne dakaren sace akwatuna. Ya nuna wani ya ce shi ne gwanin canja alkaluma a cikin kwamfuta domin a yi zurmuken kuri’u. Duk wannan an yi haka ne domin a fahimci juna, a kuma yafe musu kafin su shiga cikin sabuwar Tsintsiyar da ke tashe yanzu. A lura, irin wadannan gungun shugabannin su ne ke watayawa da neman matsayi a cikin Tsintsiya. Su ne suka kasance masu fada-a-ji cikin jam’iyyar Tsintsiya. Su ne suke jagoranci al’ummar Tsintsiya a wasu sassa na Najeriya. Su ne suke zabar wadanda za su tsaya takara, su ci zabe, su kuma mulki al’umma. Su ne suka kasance canjin da ake nema. Ina canji a nan, in dai muna aiki da kwakwalwa? Shin canji me yake nufi? Malam Aminu Kano ya fasalta mana shi ba tun yau ba. Canjin da ke da muhimmanci ko yake tabbata a cikin al’umma, shi ne wanda aka yi watsi da tsofaffin hanyoyin da ke yin tarnaki ga ci gaban rayuwar al’umma, a kama sababbin matakan da za su kawo sabuwar rayuwa da ci gaba. Amma idan an lura da kyau sai a ga cewa kamar a yanzu, shara ce ake yi cikin duhu, ba a san mai rike da Tsintsiyar ba, balle kuma abin da ake sharewa ko sharowa ko in da za a kai sharar. A cikin tsari irin wannan, tamkar wankin fararen tufa ne da ruwan tabo!