Tsintsiya ta koma lema (4)

Idan kuma wannan bai sa mu yin tunanin ta-natsu game da irin hargidiballen da ke faruwa ba, to me za mu ce game da yadda a wasu jihohin ake ta faman sa-in-sa tsakanin wadansu gwamnoni da suka ajiye Lema suka dauki Tsintsiya da sauran al’ummar da suka tarar a cikin jihar? Me yake faruwa a […]

Tsintsiya ta koma lema (4)

Idan kuma wannan bai sa mu yin tunanin ta-natsu game da irin hargidiballen da ke faruwa ba, to me za mu ce game da yadda a wasu jihohin ake ta faman sa-in-sa tsakanin wadansu gwamnoni da suka ajiye Lema suka dauki Tsintsiya da sauran al’ummar da suka tarar a cikin jihar? Me yake faruwa a jihohin Kano da Sakkwato da Adamawa da Kaduna da wasu irinsu bayan gama zabe da kuma ’yan shekarun nan da ake fafutikar sake zabe? A tuna ko kafin wadannan gwamnoni su canja sheka, akwai wadansu zaune daram a cikin sabuwar shekar da suka matsa sai sun samu wurin zama a ciki. Yanzu takaddamar ce ta yi yawa, ba abin da ake ji sai su wane ne suka dace su ja ragamar Tsintsiyar, ’yan gida na asali ko kuwa sababbin zuwa? Su wa za su zabi wadanda za su yi takara, ’yan Mowa ko ’yan Bora? Su wa za su yi takarar, ’yan asalin cikin gida ko kuwa agololi? Duk wadannan abubuwa sun dace mai bin al’amuran siyasa da kasa ya lura da su, ya kuma yi wa kansa kiyamullaili kafin a yi masa sakiyar da ba ruwa.

A cikin irin wannan kwamacala, ba ma ganin cewa za a yi abin nan ne da Hausawa ke cewa ba cinya ba, kafar baya? Ba ma jin cewa idan Lema ta saje da Tsintsiya muna nan dai yadda muke, jiya kamar yau? Ba ma jin cewa idan har tuta da alamun jam’iyya ne suka canja, to ba canji ba ne aka samu, kila sai dai caji da cuta da cutarwa?

Wani abin kara la’akari shi ne, irin yadda masu sukuwa a kan dokin da Tsintsiya ta samar suka kasance bara-gurbi a can da na tsawon lokaci. Su ne ake ce da ’yan adawa. Su ne ake zagi da ci wa mutunci. Su ne ’yan Lema ke wa kallon uku-kwabo-kosai. Su ne al’ummar kasa suke kyama don ba su ke kan gadon mulki ba. Amma yanzu komai ya ‘canja’ mai doki ya koma kan kuturi. Sai dai ina son kada mu yi saurin mantawa da irin abin da ke faruwa yanzu. A cikin bargar Tsintsiya yau, akwai wadanda tun asalinsu ’yan Lema ne, suka gudu zuwa wasu gidajen can daban, na tsawon shekaru, daga baya suka sake tarewa a jikin Lema, yanzu kuma suna ta daga Tsintsiya sama, cewa su ne masu share dattin da ’yan uwansu suka tattara. Wannan abu na iya sake faruwa nan gaba; domin ba mutanen kwarai ake nema su shigo cikin Tsintsiya ba, tarin jama’a dai kurum ake so daga Lema ko ma shadda, ba wanda ya damu. A lura da kyau ba tallata kyawawan manufofin Tsintsiya ake yi a halin yanzu ba don neman jama’a. Ba kuma ana yawo da fuskokin da za su sa talaka ya dara ba ne in ya gan su a cikin Tsintsiyar, domin ya san fuskokin tun shekarun baya a matsayin ‘gantalallu’ ko ‘gafalallu’, wadanda suka yi masa wa-ka-ci-ka-tashi, a lokacin suna wata shekar ba ta Tsintsiya ba, amma ba abin da zai iya yi sai kallo. Idan ya zura ido ya sake nazari, ya kalli fuskokin sai ya rasa gane na Tsintsiya ko Lema! barayi ko masu bin sawun barayin! Talaka ya sani, wadannan fuskoki ba su ne masu agaza masa ba, masu danne shi ne, don sun danne a baya da kyar suka daga shi ya samu yin nishi. A cikin irin wannan tsarin a duk lokacin da talaka ya daga ido ya ga wadanda ya yaka a baya domin kawo canjin a kasar nan, ga su nan tinjim a cikin Tsintsiya, dole ransa ya baci in mai son gaskiya ne. Sa’annan idan ya sake yin kallo da kyau, ya gane cewa ai yawancin Limaman Tsintsiya a da can da sun kasance limamai karkashin Lemar da ta kasa kare su daga dukan ruwan sama ko kuma bugun rana a tsawon shekaru da wuya ya aminta da duk wani holokon alkawari ko kuma canjin da kila ba zai gani a kasa ba!

Tambayar da wadansu ka iya ita ce to ina mafita daga wannan gamaden siyasa? Me talaka zai tsinkaya daga hadarin da ya hadu a yanzu a cikin sararin samaniyar siyasar kasar nan, daga yanzu zuwa nan gaba har zuwa zaben 2019? Me talakan Najeriya ya kamata ya yi ko ya sani dangane da irin wannan harbar-ta-Mati da ake yi ko ake neman a yi masa dangane da shugabancin kasar nan? Sa’annan uwa-uba wace rawa ce zai iya takawa wajen kawo wa kansa da kasa canjin da ya dace da ita, idan al’amurra sun ki ci, sun ki cinyewa?

kila amsa irin wadannan tambayoyi ba daga gare ni ya kamata su fito ba, amma kuma muna iya hada karfi da karfe waje daya mu ga ko za mu iya samar da mafita daga wannan hargidiballe. Sai dai kafin mu yi nisa mu fahimci wani abu guda da ke da muhimmanci. Najeriya a matsayin kasarmu, ta kowa da kowa ce, daga shugabannin har zuwa wadanda ake shugabanta, ke nan ba wani da zai ce shi ne ya mallake ta, saboda haka shi ne zai yi mata alkiblar da yake ganin ita ta dace da ita. Shugabannin siyasa suna bisa matsayi ko mukaman da suke kai ne a matsayin wakilai na sauran al’umma, saboda haka don mun zabe su ko sun samu kansu a bisa irin wannan matsayi ba yana nufin an ba su lasisin da za su yi yadda suka ga dama ba ne, dole ne su yi aiki domin al’umma ba domin kyautata wa kansu ko wadansu ’yan tsiraru ba. Idan haka ne tsarin ya tanada, wanda kuma hakan ne, ke nan mulki a hannun al’umma yake ba wadanda aka zaba ko suka samu kansu bisa kowane irin matsayi ba.

A bisa irin wannan tunani, abubuwan da suka dace mu mayar da hankali kai a cikin irin wannan tarmahaha ta Lema da Tsintsiya da kuma tafarkin ciyar da kasa gaba da yi wa al’umma aiki da kuma ingantaccen tsarin siyasa su ne mu koma bisa turbar yin aiki domin al’umma daga mutanen da al’umma suka amince da su a matsayin natsattsu, kamilai, yardaddu, masu hangen nesa da neman mafita ga al’umma. Kada in ji wani ya ce ai ba mu da su, domin kuwa suna nan jibge a cikin tsibin mutanen da ke cikin kasar nan, sai dai ba mu damu ko ba mu kula da nema da hulda da su ba ne, ganin cewa sankara ta kame kowane bangare na rayuwar yau da kullum ta ’yan Nijeriya.

Za Mu Ci Gaba