Tsintsiya ta koma lema (5)

Me nake so mu yi ke nan? Mu yi watsi da jam’iyya mu kama gaskiya! Wacce ce gaskiyar? Gaskiya irin ta marigayi Aminu Kano, irin ta marigayi Obafemi Awolowo, irin ta tsohon Gwamnan Kaduna, Abdulkadir Balarabe Musa, gaskiya irin ta Janar Muhammadu Buhari da irin su da dama a cikin kasar nan. Duk da cewa […]

Tsintsiya ta koma lema (5)

Me nake so mu yi ke nan? Mu yi watsi da jam’iyya mu kama gaskiya! Wacce ce gaskiyar? Gaskiya irin ta marigayi Aminu Kano, irin ta marigayi Obafemi Awolowo, irin ta tsohon Gwamnan Kaduna, Abdulkadir Balarabe Musa, gaskiya irin ta Janar Muhammadu Buhari da irin su da dama a cikin kasar nan. Duk da cewa ire-iren wadannan mutane da na lissafo suna da jam’iyyun siyasa da suke tokabo da su, za a samu cewa su din ne jam’iyyun siyasar, ba siyasar ce su ba! Manufofi da tadoji da kimar siyasar na tattare da su da mabiya bayansu a koyaushe. A duk lokacin da suka fadi zance ko suka yi alkawari al’umma na amincewa da su domin sun san su da gaskiya da rikon amana. Shi ya sa a siyasar irin wadannan mutane ake ganin karancin jam’iyya tattare da su, amma kuma suna samar da yawaitar mutane na kwarai daga jikinsu.

A zamanin su Aminu Kano da Jam’iyyar Makulli/Mabudi da Gida da Masara, kowa ya san matsayin kowace jam’iyya, musamman a nan Arewaci Najeriya. Haka abin ya kasance a zamanin NEPU da NPC a zamanin su Sardauna. Mutane su ne jam’iyya, su ne gwamnati, su ne kuma masu fada-a-ji, saboda kowace jam’iyya da manufofin da suke jan ra’ayin al’umma zuwa gare ta, su kasance tare da ita komai runtsi, ba haka nan suke kara-zube ba.

Irin wannan ne ya gina so da kaunar Awolowo ga mutanensa, haka kuma irin su Balarabe Musa da kuma yanzu Janar Muhammadu Buhari. Har yau din nan, abin da Balarabe Musa ke kira ga al’umma shi ne, kowa ya bar batun Tsintsiya da Lema ya koma ga Mabudi/Makulli a matsayin mai ceto da cetarwa. Ba wani abu ya sa yake furta haka ba, domin ya san cewa manufofin PRP da ya dage kai; su ne za su iya fitar da kasar daga cikin halin  kaka-ni-ka-yi, sa’annan uwa-uba ba kowa ba ne zai iya aiwatar da manufofin, sai mai gaskiya. Wannan shi ne gaskiyar zance, kuma shi ne muke gani a tsarin siyasa irin ta Janar Buhari, wadda kuma jama’a da kansu ke fada tun daga 2003 zuwa yau game da shi da wadansu. Shin jam’iyya ce ta sa ake son shugabancin Janar Buhari a wasu sassan kasar nan? Shin jam’iyya ce ta sa ake kewar Bola Tinubu a inda yake a Najeriya? Shin jam’iyya ce ta sa ake yabawa da ayyukan Rabi’u Musa Kwankwaso, a lokacin yana Gwamnan Kano ko Fashola a lokacin yana Gwamnan Legas? Ko alama! Ba ruwan jam’iyya, in ma akwai ruwan jam’iyyar a wasu wurare to shugaba shi ya fi damawa, domin ya yarda da abin da yake yi, jama’a kuma sun aminta da shi; kuma zai gabatar da aiki ko da jam’iyya ko ba jam’iyya, domin aikin ya zo yi ba sharholiya ba. Wanda shi ke da muhimmanci.

Wannan ne ya sa tunda ake ta fafutikar kawo sauyi a kasar nan, amon da ya fi tashi, musamman a nan Arewa shi ne, ba a son kowa ‘Sai mai gaskiya!’ Ba wanda ke cewa sai ‘Jam’iyya mai gaskiya,’ in ma an ji wadansu sun fadi haka, to saboda mai gaskiyar ne, ba don komai ba, domin a yawancin tunanin mutane ba ruwansu da wannan jam’iyya, sai mai gaskiya. Idan da muna da gaskiya ko aiki da ita da ba mu ga tambelen da wadansu ’yan siyasar ke faman yi daga wannan jam’iyya zuwa waccan ba, ba matsaya guda, sa’annan a ce kuma ana neman canji. Idan ba a yi hankali ba duk sai an koma cikin Lema cikin wayo ko kuma dabara, a yi ta shara, mai tada kura, sa’annan a ce canji ake nema!

Gaskiyar batu ita ce, ba mu da jam’iyyu sai masu murkushe al’umma da sunan jam’iyyun, suna kuma yin haka ne ganin cewa sai da jam’iyyun ne kurum za a iya takarar zabe, a ci zaben ko kuma a ce an ci zabe. Ba su damu da zabar wadanda za su bauta wa al’umma ba, in har sun zabo wadanda ke da kishin kasa da son al’umma su yi shugabanci to kila cikin rashin sani ne ko mantuwa, kuma an rika samun takun-saka tsakanin shugaban da wadanda suka dora shi ko ita. A irin wannan tsari ba abin da ya rage sai a koma ga tsarin da hankali zai iya karba, kuma zuciya na so. Wane ne wannan tsarin?

Tsarin nan shi ne tsarin da talakawa ne ke jan ragamar siyasa da ’yan siyasar. Tsari ne da mutanen kasa su ne jam’iyya ba wadansu ’yan tsirari da ke hayewa kan akawal ko dandan mulki su ce su ne masu fada-a-ji ba. Tsari ne da al’umma za su ce ga yadda suke so a yi, a kuma tabbata an yi, ana so ko ba a so! Tsari ne da ke nuni zuwa ga tafarkin ci gaba, ba tafarkin cika aljihu da zama ’yan ma’abba ba. Wannan tsari ba wani tsari ba ne da ya wuce al’umma ta yi wa kanta kiyamullaili, su zabi mutane nagari domin su jagorance su, ko da kuwa daga jam’iyyar Shaidan suka fito, in dai sun tabbata su ne mafita ga al’ummar. Sai dai a lura, in an zabi irin wadannan mutane to ya dace kuma a tabbata ana bin su da hajar mujiya a koyaushe, domin a tabbatar ba su kauce wa hanya a kowane mataki na mulki da jagorancin al’umma ba.

Ta yaya hakan zai iya kasancewa? Mu sani a yau ba mu da zabi a tsakanin Tsintsiya ko Lema ko wani abu makamancin haka, domin kuwa duk kanwar ja ce. Wanda yau ya kasance dauke da Tsintsiya gobe kana iya ganinsa a cikin Lema, kuma ya yi maka kiri-da-muzun cewa nan ne matattarar alheri. Haka wani na iya gajiya da zama cikin inuwar Lemar, ya fito cikin rana gatsar ya fara shara da Tsintsiya ya ce maka ai ba komai cikin Lemar sai kyankyasai da bara-gurbi, alhali kuwa nan inda yake zaune da Tsintsiyar bara-gurbin sun fi yawa, kyankyasai kuwa tuni suka yi gida suka zaune!

Dangane da haka ni a tawa tsinkayar akwai abubuwa kamar guda hudu da za mu iya yi ko matakan da za mu iya bi domin kaiwa ga tudun-mun-tsira. 

Za mu ci gaba