Tsinuwar Na Nan!: Martani (1)
Yau kuma zan ba masu karatu fagen ne domin su amaye cikinsu game da bayanan da na kawo game da Tsinuwa da Najeriya a makwannin baya. An yi haka ne domin a samar da kafa ta musayar ra’ayi da masu karatu, domin a harkar irin wannan dole ne a samu mutane da ke amincewa da […]
Yau kuma zan ba masu karatu fagen ne domin su amaye cikinsu game da bayanan da na kawo game da Tsinuwa da Najeriya a makwannin baya. An yi haka ne domin a samar da kafa ta musayar ra’ayi da masu karatu, domin a harkar irin wannan dole ne a samu mutane da ke amincewa da batutuwa da kuma masu akasi. Ga fili ga doki!
Sani Audi: To yanzu abin ya juya. Wancan lokacin za ka ga iyaye ke tsine wa ‘ya’yansu, amma yanzu talakawa ne ke tsine wa masu mulki, shi ya sa ka ga komai ya kasa gaba, ya kasa baya. Allah Ya kyauta kawai za mu ce.
Mustapha Dankano: Wannan abin tunani ne mai zurfi Malam, domin kuwa in ka je Kudancin kasar nan ma hakan take, abu kadan sai ka ji ance, If na lie make God punish you, su kuma ta su tsinuwar ke nan a wajen su. Da fatar Allah Ya shirye mu baki daya. Allahumma Amin ya Rabbi.
Kujama Soofee: Akwai alamar wannan tsinuwa a kan Najeriya, sai dai abin da ya buya muke jiran Malam ya bankado, shi ne wanda ko wadanda suka tsine wa kasar da kuma sanda tsinuwar ta soma aiki tare da inda aikin na ta zai balbale. Allah Ya kiyashe mu da tsinace-tsinace.
Ahmad A Daura: To ga dukkan alamu dai ana nan jiya, i yau, karatun kurma da makaho ba mai fahimtar wani bare a samu ci gaba. Shi ya sa al’amurran suka taru suka rincabe, aka rasa gane in da za a dosa, rana zafi, inuwa kuna. Fatar mu Allah sa wadanda suka yi wannan tsinuwa su dawo su warware ta ko da ta hanyar yin azumin kaffara ne don Najeriya da ‘ya’yanta su samu sa’ida, su ma su samu romon jin dadin da uwa mai nagartattun ‘ya’ya ke samu. Idan kuma uwar ce, ita Najeriyar ke nan ta yi fushi da ‘ya’yan na ta, to mun tuba, ta yi hakuri, ta yafe wa ‘ya’yanta. Shi hannunka idan ya samu matsala kokarin nema masa magani ya kamata ka yi, maimakon ka yanke ka yar.
Abdullah H. Ibrahim Majia: Allah ya ganar da mu a kan cewar tsinuwa ba ita ce mafitarmu ba.
Dauda Yahaya Ango Makarfi: Wannan gaskiya ne, mafita yanzu kawai a koma ga Allah ai ta istingifari.
Haruna Muhammed Idris: Rashin yin abin kirki ko zalunci ko cin amana ko ha’inci suke sa tsinuwa ko a da yaro azzalumi ko maha’inci ko mara tausayin iyaye shi ke cikin matsala. A yanzu kuwa shugabanni su ne azzalumai, maciya amana. Kullun burinsu yin zalunci da karya da yaudara. Ya za a yi talaka ba zai fusata ba. Laifin ai nasu ne.
Sada Rumah: Mummunan furuci ga Shugaba tamkar tsinuwa ce da kan sa ya sangarce, ya dinga kuzar talakawa, su kuma su yi ta kururuwa da Allah Ya isa. Don haka, kyakkyawan zato da addu’a ce mafita. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, duk wanda ya sayi rariya. …! Ke nan ana yabon Ciwake Sallah, amma ya kasa tada Bisimilla, bare fatiha!
Muhammad Abdullahi Katsina: Kamar yadda ka ce kowa ya gyara domin gaskiya ba masu mulkin kadai za su gyara ba, har da mu wadanda ake mulkar, sai mun gyara.
Babbar matsalar Farfesa, ni a nawa dan karamin kukumin sanin, sai na ga da masu mulkin da wadanda ake mulka duk ba su shirya wa mulkin ba, domin kuwa shi mulki idan har ka yi niyyar yin shi to sai fa ka sadaukar da komai naka ka fuskanci wannan mulkin kawai. Haka shi ma wanda ake mulka, sai ya sadaukar da komai domin a mulke shi. To inda matsalar take, su masu mulkin kawunansu kawai suke azurtawa da dukiyar al’umma, su kuma wadanda ake mulkar ba sa iya jure radadin da suke fuskanta da jawo hankulan masu mulkin na su, shi ya sa a kullum an kasa ci gaba, jiya iya yau. Fatarmu Allah Ya dubi lamarrammu ya cece mu daga hannun ‘yan ba ni na iya. Amin.
Sada Bin Suleiman Usman: To da wuya in ba tsinuwar da talakawa ke yi wa shugabanni ba ce ta ke neman hargitsa mana kasa ba.
Muhammed Ibrahim: Farfesa, wannan rubutun ya kara tabbatar da Farfesancinka a wannan fanni. Domin a cikinsa, cikin hikima ka kunshe darasin tauhidi da kuma amfanin kyautata wa iyaye, ka ajiye wa natsatstsen mai karatu don ya dau darasi. A lokaci guda kuma jigon rubutun na nan a a gaban mai karatu yana kallonsa, duk da ba ka ida bayyana shi ba, amma dai bai buya daga idon mai karatun ba. Wannan hikima ce, zurfaffa ta manyan malamai. Wallahi ina alfahari a ce kawai na san ka. Allah ya kara girma da koshin lafiya da wadata da tsawon rai, a wannan rayuwa taka wadda ta dace da ruwayar Manzo (SAW) da ke cewa mafi alherin mutane shi ne wanda ke amfanar da su.
Jamilu A Hasheem: Allah Ya kyautata ayyukan malam, ya kara yi wa rayuwa tagomshi nan duniya da can lahira. Amin. Allah gafarta Malam bisa wannan dan ta’aliki da ka yi, da alamun tsinuwar ce yanzu ta sami fadawa kan shugabanni suka zama tatattu wajen iya karya da yaudara da kuma kokarin tara wa ‘ya’yansu abin duniya, saboda wai, kar su mutu su bar su a talauci. Allah Ya kyauta, Ya kuma sa mu sauya furucin labbanmu. Amin.
Muhammad Sanee Bauchi: Allah Ya shirye mu, Ya yafe mana, Ya ba mu mafita, amin.
Hasheem Sa’eed Yahuza: Allah Ya sa mu cikin hanya madaidaiciya,wato kala lahu, kala rasulu, kala tabi’un. Allah Ya sa mu dace…..Astagafurullahu wa’a tubu ilaikah.
Salmanu Lawal Danja: Farko an saki reshe ne an kama ganye, sa’anan ko wane mutum da irin tarbiyar da ya samu da ita yake tashi, su kuma wadanda suke yawo suna ihu ko shaye- sheye, kakan ki naka ne, duniya ta so shi, ka so shi duniya ta ki shi, sa’anan su ma masu madafun iko suna kula da nasu ‘ya’ya a gida, sun bar ‘ya’yan talakawa a zube. To sai dai addu’a kurum. Mun gode.
Za Mu Ci Gaba