Tsinuwar na nan!: Martani (2)
Hauwa Hussain Muhd: Kalamai daga bakin masu ilmi sun fita daban. Allah Ya kara lafiya da nisan kwana mai girma Farfesa. Isyaku Hassan: Allah Ya datar da mu da alheri, amma akwai aiki ja a gabanmu. Sunusi Tijjani Kwari: Hmmm! Gaskiya malam ya yi jawabi mai matukar mahimmanci, kuma zahiri abin da ya fada haka […]
Hauwa Hussain Muhd: Kalamai daga bakin masu ilmi sun fita daban. Allah Ya kara lafiya da nisan kwana mai girma Farfesa.
Isyaku Hassan: Allah Ya datar da mu da alheri, amma akwai aiki ja a gabanmu.
Sunusi Tijjani Kwari: Hmmm! Gaskiya malam ya yi jawabi mai matukar mahimmanci, kuma zahiri abin da ya fada haka yake. Sai dai mu ce Allah Ya sa mu gyara wannan halayyar tamu.
Rabiu Isah Hassan: A ganina ba tsinuwa ba ce ke yawo a kanmu ba. Tun farko Najeriyar ce ba ta yi ba. Akwai wasu sunnoni da kasashe suka siffantu da su da mu muka saba, shi yasa.
Al’Mansoor Gusau: Farfesa, Allah Ya kara lafiya, wannan ba tsinuwa ba ce, halayenmu ne. Kuma wallahi! ba a shirye muke da mu gyara ba, saboda son zuciya. Galibinmu abin da ke bakinmu ba shi ne a zuciyarmu ba. Shugaba Buhari ya ce “Canji ya fara daga kaina” Mutane sun dauki wannan maganar wasa ce, ba karamar magana ba ce. Wallahi! Sai kowanenmu ya gyara kura-kuransa, sannan mu ga canji.
Asmau Ahmad: Haka ne fa sai mun gyara zukatanmu sannan za mu gyaru. don gaskiya muna da son kammu da yawa. Kowa ya samu sai zalunci, daga shi sai matarsa, sai ’ya’yansa ’yan uwa, ba kowa ke kula da su ba sai wadda Allah Ya ba wa mata tagari, saboda haka ba tsinuwa ba ce.
Sulaiman Aliyu Zango: Alkalami a hannun manya, ga ilimi, ga shekaru. Na san wannan kan ne, gangar jikin na baya. Allah dai Ya sa mun fahimci fikihun Malam na hasko mana mizanin tsinuwa daga idon yaran jiya. Ya manyan yau suka dauke ta, bare yaran yau? Tuni ’yan amin sun amsa tofin ’yan kasar ga shugabanninmu da kasarmu.
Mu matasa ire-iren wannan karatun na Farfesa ya kamata a nada. Domin akwai sauran kallo a Najeriya ga masu tsawon numfashi.
Salisu Maladi Darazo: Allah kara tsawon rai da basira, muna bukatar rubutunka, Malaminmu, Abin alfaharinmu.
Haruna Muhammed Idris: Rashin yin abin kirki ko zalunci ko cin amana ko ha’inci suke sa tsinuwa ko a da yaro azzalumi, maha’inci, mara tausayin iyaye shi ke cikin matsala. A yanzu kuwa shugabanni su ne azzalumai maciya amana, kullum burinsu zalunci da karya da yaudara, ya za a yi talaka ba zai fusataba. laifin nasu ne.
Sada Rumah: Mummunan furuci ga shugaba tamkar tsinuwa ce da kan sa ya sangarce, ya dinga kuzar talakawa, su kuma su yi ta kururuwa da Allah Ya isa. Don haka kyakkyawan zato da addu’a ce mafita. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, duk wanda ya sayi Rariya….! Ke nan ana yabon Ciwake Sallah, amma ya kasa tada Bisimilla, bare fatiha!
Haruna Muhammed Idris: Kullun karya suke ma talaka, ba sa tausayinsa. Akwai talakan da bai taba sayen keke ba, su motoci nawa suke hawa, su da iyalansu? Ya abincinsu yake? Makarantu fa? Kiwon Lafiya fa? Muhalli fa? Don haka kowa ya gyara.
Muhammad Abdullahi Katsina: Kamar yadda ka ce kowa ya gyara to gaskiya ba masu mulkin kadai za su gyara ba, har da mu wadanda ake mulkar sai mun gyara. Babbar matsalar Farfesa ni a nawa dan karamin kukumin sanin, sai na ga da masu mulkin da wadanda ake mulka duk ba su shirya wa mulkin ba, domin kuwa shi mulki idan har ka yi niyyar yin shi to sai fa ka sadaukar da komai naka ka fuskanci wannan mulkin kowai. Gyara na hannun mu.
Sada Bin Suleiman Usman: To da wuya in ba tsinuwar da talakawa ke yi wa shugabanni ba ce take neman hargitsa mana kasa ba.
Muhammed Ibrahim: Farfesa, rubutun nan ya kara tabbatar da farfesancinka a wannan fanni. Domin a cikinsa, cikin hikima ka kunshe darasin tauhidi da kuma amfanin kyautatawa iyaye, ka ajiye wa natsatstsen mai karatu don ya dau darasi. A lokaci guda kuma jigon rubutun na nan ga mai ganewa.
Jamilu A Hasheem: Allah Ya kyautata ayyukan Malam, ya kara yi wa rayuwa tagomashi a duniya da lahira. Allah gafarta Malam bisa wannan dan ta’aliki da ka yi, da alamun tsinuwar ce yanzu ta sami fadada kan shugabanni suka zama tatattu wajen iya karya, da yaudara, da kuma kokarin tarawa ’ya’yansu abin duniya. Saboda, kar su mutu su bar su da ralauci… Allah Ya kyauta, Ya kuma sa mu sauya furucin labbarmu.
Hasheem Sa’eed Yahuza: Allah Ya sa mu cikin hanya madaidaiciya,wato kalaLlahu, kala rasulu, kala tabi’un. Allah Ya sa mu dace…..Astagafurullahu wa’a tubu ilaika.
Salmanu Lawal Danja: Farko an saki reshe ne an kama ganye, saannan ko wane mutum da irin tarbiyyar da ya samu da ita yake tashi, su kuma wadanda suke yawo suna iho ko shaye- sheye, kakan ki naka ne duniya ta so shi, ka so shi duniya ta di shi. Sannan su ma masu madafan iko sun tsane nasu a gida sun bar ’ya’yan talakawa a zube to sai dai addu’a kurum Mun gode.
Abdurrazak Suleiman: Allah ya ja zamanin babban maigidanmu, ai da duk da lalacewar shugabanni na baya suna da ’yan hanyoyin da suke taimakawa talaka, kamar su tallafin fetur, tallafin taki, tallafin dala, tallafin aikin hajji da rashin matsawa wajen amsar haraji, yanzu fa?
Abdullahi Garba Jani: A koda yaushe, babu abin da ke ran kakanni da iyaye da ’ya’ya da jikokin Najeriya sai zakuwar ganin kasar ta koma turbar da aka santa a kai, wato ta ciyar wa da shayar da wadanda nauyinsu yake kanta.
To amma, wani abu mai kama da hawainiya, shi ne abubuwa sun canza, Allah kadai ne magani.
Rabiu Isah Hassan: Babu wata tsinuwa a kan Najeriya. Sai dai ba zan yi mamaki ba idan wasu sun dauka tsinuwa ce ke yawo a kan kasar, saboda kullum gwanda jiya, i yau. Tunanin tsinuwa tsohon al’amari ne a tarihin duniya. Shi ya sa har ake da kissar Annabi Nuhu da ’ya’yansa uku da aka ce ya tsine wa.
Tijjani Abba: Allah Ya sa wannan sharhi ya zama silar zaburar da mu, domin yunkurin lalubo makarin wannan tsinuwa. Allah Ya saka wa shaihin Malami da mafificin alheri.
Muh’d Jameel: Ba za mu gajiya ba wajen bibiyar abin da Shehun Malami yake son amayarwa, domin mu amfana da shi ba. Allah Ya sa kar ka gaji Malam, ya kuma kara wa rayuwa albarka.
Fatima Musa Hamza: Hmm!! Wani aiki sai masu hangen nesa. Dama ita masifa ko jarabta ko annoba, takan shafi wadanda ba su ji ba, kuma ba su gani ba ne. Ko shakka babu dama abin da ya je ai shi yake dawowa. Allah dai Ya sa mu canza ko za mu ga da kyau.
Bashir Kabir Kutawa: Hum! Najeriya kasarmu ta gado. Allah dai Ya fitar da A’i ga rogo. Allah kuma Ya saka wa Shehin malami da alheri.
Rabiu Isah Hassan: Kayya! Fahimta ta ta saba da taka. Abin tambayar ma wa ya tsine wa Najeriya? Me ta yi aka tsine mata? Yaushe aka tsine mata? Yaushe tsinuwar nan ta fara kama ta? Kamar yadda na yi alkawari a baya, ba zan kawo fahimtata a kan matsalar Najeriya ba har sai an kare.
Nura A Hussaini: Wannan falsafar zance ce kawai, amma ba wai Farfesa na nufin tsinuwa ta baki ba ne, ko ta wani babba ba. A’a, tsinuwar a aikace aka yi ta.
Aliyu A. Wali: Muna kara mika godiya ga Farfesanmu! Allah Ya yi jagora ya sa albarka. Mun gode!
Suleiman Umar: Daga 1999 zuwa 2015 Najeriya ta kara samun wani arzikin amma ’ya’yanta suka shiga wawasu da nuna cewa kowa ya san gidan ubansa da danginsa ne kawai, kila shi ya kai ga wasu dangin ke son ballewa, wasu kuma saboda an hana su yin wandaka da dukiyar uwarsu suke neman kassara dan abin da ya rage mata da satar wasu ’ya’yan don neman kudi da dai sauran abubuwan assha na kashe-kashen ’yan uwa.