Tsiron Soyayya

Assalamu alaikum wa rahmatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah SWT Ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo cikinsa, amin. A yau inshaAllah wani dan karamin kwas ne za mu gabatar ga ma’aurata kan ilmin soyayya don su fahimce ta, ta haka za su fi samun saukin bayyanawa […]

Tsiron Soyayya
Tsiron Soyayya

Assalamu alaikum wa rahmatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah SWT Ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo cikinsa, amin. A yau inshaAllah wani dan karamin kwas ne za mu gabatar ga ma’aurata kan ilmin soyayya don su fahimce ta, ta haka za su fi samun saukin bayyanawa da aikatar da soyayyarsu ga junansu. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Soyayya…
Kalmar soyayya na nufin samuwar kyawawan shau’ukan so, kauna da fatan alheri cikin zuciya, wadanda za a bayyanar da su a aikace ta hanyar nuna kulawa, kyautatawa da tausayawa ga wanda ake son, da kuma kokarin samar da jin dadi da farin ciki; da kore bakin ciki da wahala. Soyayyar auratayya kuwa ita ce dunkulalliyar kuma cikakkiyar kulawar ma’aurata ga junansu ta hanyar samar da wadancan abubuwa da aka ambata a sama. Daga wannan bayanin muna iya fahimtar cewa soyayya wata itaciya mai rassa guda biyu muhimman juna: reshen farko na dauke da kyawawan shau’uka cikin zuciya a badinance, reshe na biyu na dauke da aikatar da wadannan shau’uka a zahirance.
dan Tsiron Soyayya
Wadannan su ne abubuwan da suke tsirar da shaukin soyayya cikin zuciya, kowannensu na da muhimmanci wajen tallafar soyayya, sannan irin yanayin inganci da karfin tsiron, irin yanayin sakamakon soyayyar da za ta bayyana; in kuma tsiron ya samu nakasu, to zai haifar da nakasu ga soyayyar da ya tsirar. Tsiro daya na iya tallafar soyayya har ta kammala matukar bai samu nakasu ba, amma da ya samu nakasu to zai yiwu ma a nemi soyayyar a rasa. Don haka kammalalliyar soyayya, wacce ke iya jure kowane irin yanayi, ita ce wacce ke kunshe da dukkanin dan tsiron nan da bayaninsu zai gabata:
1.    kauna
kauna ita ce tsiron farko da ke haifar da soyayya, kuma ta kasance tsabtataccen shauki ne da ya samo asali bisa wani dalili tsabtatacce kuma abin burgewa ga zuciyar da take kaunar. kauna ta kasu gida biyu:
1.    Tabbatacciyar kauna itace wacce ba ta taba daukewa daga cikin zuciya komai daren dadewa; wannan ita ce irin kaunar da muke yi wa ‘ya’yanmu, iyayenmu da ‘yan uwanmu. Komai ya faru na yanayin rayuwa, ba ya iya tumbuke tsiron kaunar gaba daya daga cikin zuciya. Tabbatacciyar kaunar da ta yi zarra a wannan bangaren ita ce kaunar uwa ga danta, domin akwai yiwuwar kaunar iyaye da ‘yan uwa ta ragu ko ta karu a dalilin faruwa ko rashin faruwar wani abu, amma kaunar uwa ga danta ba ta taba raguwa cikin zuciya.
2.    kauna marar tabbas ita ce kaunar da ta faru a bisa wani dalili mai canzawa: da zarar dalilin ya canza, to kaunar ma za ta canza ko ta dauke gaba daya; wadannan sun kunshi:
•    Mallaka: Mallakar wani abu mai kyawu kuma mai alfanu ga mutum na tsirar da kaunar abin nan cikin zuciya; wannan ne ya sa muke kaunar ma’auranmu da dangi mafiya kusanci.
•    Kyautatawa/kulawa: duk zuciya na kaunar mai kyautata mata, domin ita kyautatawa alama ce ta nuna kauna.
•    Kyawun Hali: wata kaunar na tsira ne a dalilin kyaun hali da irin yadda halin ya burge zuciya.
2.    Sabo:
Duk lokacin da mutum biyu suka saba da juna, kullum suna haduwa suna tare, ko suna yawan haduwa ko suna yawan aiwatar da wani abu tare, dole ne kaunar juna ta kullu a tsakaninsu. Shi ma sabo, ya kasu kashi biyu ta yadda yake tsirar da soyayya, sabon da aka yi shi hade da fahimtar juna shi ke haifar da sahihiyar soyayya da mutunta juna, sabon da aka yi shi ba fahimtar juna, ba ya haifar da soyayya sai dai a ce masa sanayya kawai.
3.    Tausayi
Shi ma yana tsirar da soyayya cikin zuciya, in shaukin tausayi ya bayyana cikin zuciya to yana nannade da shaukin soyayya, duk wanda ake tausayi, to tabbas ana son shi.
4.    Aminta
Yarda da Amincewa tsakanin mutum biyu na tsirar da soyayya da kaunar juna cikin zuciyarsu, haka kuma rashin yarda da aminta na tsirar da rashin soyayya.
5.    Sha’awa
Sha’awa ta kasance tana tsirar da gawurtacciyar soyayya lokacin da take kan ganiyarta, domin tana samar da dukkan sauran kayan hadin soyayya, musamman kyawawan shau’ukan jin dadi da sha’awar saduwar auratayya. Sai dai sha’awa shaukin bogi ne domin ba ta da tsawon rai cikin auratayya, don haka soyayyar da sha’awa ce ta tsirar da ita, to karar kwananta kusa yake sai in har an tallafe ta da wasu daga cikin sauran kayan hadin soyayya.
6.    Shakuwa
Wannan ita ce babbar jigon soyayya, domin cikin shakuwa, akwai kaunar juna, akwai sabo, kuma akwai yarda da amincewa, sannan kasancewar shakuwa cikin dangantakar ma’aurata, na tsirar da tabbatacciyar sha’awa a tsakaninsu. Dukkan sauran tsirran soyayya kan iya samun nakasu a cikin zuciya a bisa wani dalili, kuma da sun samu nakasu, to soyayyar ma za ta samu nakasu, amma shakuwa tabbatacciya ce cikin zuciya har abada, ba a taba dawowa a ce babu wannan shakuwar.
Sai sati na gaba insha Allah za mu ci gaba. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulwarSa a kodayaushe, amin.