Tsofaffi ne matsalar Najeriya – Jonathan
Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya zargi tsofaffin ’yan Najeriya da haifar da matsalolin da ke damun kasar nan, a sanadiyyar kalaman da suke furtawa da irin dabi’unsu. Shugaban ya yi wannan zargin ne a ranar Talatar makon nan. Shugaban kasar ya furta cewa matasan Najeriya ne ke ci gaba da jawo wa kasar nan daukaka.Ya […]
Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya zargi tsofaffin ’yan Najeriya da haifar da matsalolin da ke damun kasar nan, a sanadiyyar kalaman da suke furtawa da irin dabi’unsu. Shugaban ya yi wannan zargin ne a ranar Talatar makon nan.
Shugaban kasar ya furta cewa matasan Najeriya ne ke ci gaba da jawo wa kasar nan daukaka.
Ya dai soki lamirin tsofaffin ’yan siyasar kasar nan, wadanda ya ce suna haifar da rikici, ta hanyar fada da aibata juna.
Jonathan ya yi wannan maganar ne a lokacin da ya kaddamar da shirin samar da aikin yi ga matasa a fannin noma da kuma Asusun bunkasa noma a Najeriya, wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ya ce: “Matasanj Najeriya maza da mata, wadanda muke gani a yau, da wadanda ke waje, muna mika godiya da yabo a gareku, saboda daukacin abubuwan da kuke yi, suna haifar wa kasar nan da daukaka.
Su kuwa tsofaffin mutane irin mu, duk abin da suke yi, a kodayaushe yana haifar da matsala.
“Ana damawa da matasa a harkokin wasanni da kwallo da tsalle-tsallen motsa jiki da suransu, kuma tsakanin lokacin da nike mataimakin shugaban kasa, har na zama shugaban kasa, suna ta jawo mana daukaka.
“Akwai amtasa a harkokin fina-finai, wadanda aka fi sani da Nollywood, shi ma wannan wania bin farin ciki ne a gare mu.
“Matasan sun shiga harkokin kade-kade da raye-raye, kamar su D-Banj, kuma suna cus amana annashuwa.
“Amma idan aka yi la’akari da tsofaffi irin mu, sai a ga mun yi dumu-dumu wajen fada da aibata junanmu, al’amarin da ke haifar matsala ga ’yan Najeriya wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.
“Don haka muke da tabbacin cewa ci gaban kasar nan yana hannun matasa. Tabbas matasan ’yan Najeriya za su kai mu ga gaci, zuwa inda muke nufin kaiwa.
“Wata rana za su kai mu zuwa duniyar wata. Ina da tabbaci game da fasaha da basirar matasa. Tabbas za mu samar da yanayi mai kyau a gareku, don kyakkyawar makomar kasar nan na hannunku, kuma za ku daukaka kasar nan.”