Tsofaffi ’yan Boko Haram sun shiga hannu

Wadansu tsofaffi uku sun shiga hannun a Jihar Yobe, inda suka yi ikirarin cewa suna yi wa mayakan Boko Haram kiwon dabbobi.  Biyu daga cikin tsofaffin ’yan uwan juna ne, yayin da daya ke cikin mutanen da sojoji suka buga hotunansu suna nemansa ruwa a jallo.An kama mutanen ne a daidai lokacin da suke kokarin […]

Tsofaffi ’yan Boko Haram sun shiga hannu
Tsofaffi ’yan Boko Haram sun shiga hannu

Wadansu tsofaffi uku sun shiga hannun a Jihar Yobe, inda suka yi ikirarin cewa suna yi wa mayakan Boko Haram kiwon dabbobi.  Biyu daga cikin tsofaffin ’yan uwan juna ne, yayin da daya ke cikin mutanen da sojoji suka buga hotunansu suna nemansa ruwa a jallo.
An kama mutanen ne a daidai lokacin da suke kokarin sayar da wasu dabbobi domin samar wa ’yan ta’adda na Boko Haram kudin sayen abinci da sauran kayan masarufi don bikin Babbar Sallah da za a yi a ranar Litinin.
daya daga cikin tsofaffin mai suna Muhammed Bulama, shi ne mutum na 105 a jerin hotunan da Rundunar Sojin Najeriya ta fitar na manyan ’yan Boko Haram da ake nema.
Bulama da yayansa, Ardo Abba Muhammed da kuma Muhammadu Kaigama sun shaida wa sojojin cewa aikinsu shi ne kula da dukkan shanu da tumaki da dawakin da ’yan Boko Haram suka sato ko suka kwace daga jama’a.
Wata sanarwa da Kakakin Sojin Najeriya, Kanar Sani Usman Kuka-Sheka ya fitar ta ce Bulama ya gano hotonsa a cikin jerin mutanen da ake nema kuma ya tabbatar da cewa shi cikakken dan Boko Haram ne.
Sanarwar wadda aka fitar a ranar Talata ta ce  an kama Muhammed Bulama da Ardo Abba Muhammed (yayan Bulama kamar yadda suka ce) da Muhammadu Kaigama a kauyen Azare da ke karamar Hukumar Gujba a Jihar Yobe tare da taimakon ’yan kato-da-gora da ke kauyen.
Sanarwar ta ce:  “An kama su ne a kan dawaki da keke suna kora wasu tumaki zuwa kasuwa. A yayin binciken farko, wanda ake zargin ya tabbatar da hotonsa a cikin mutanen da sojoji suke nema, kuma daga baya ya bayyana cewa ya kware wajen kiwon shanu ga kungiyar ’yan ta’addan.”
Sanarwar ta kara da cewa: “Ya kara bayyana cewa sun je kauyen ne domin su sayar da dabbobi saboda kudi ya kare musu a maboyarsu, kuma za su sayi abinci su koma domin shagulgulan Sallah mai zuwa.”