Tsofaffin daliban Kwalejin Makwa za su kafa kungiya don farfado da ilimi

Tsofaffin daliban Kwalejin Makwa da ke sassa daban-daban na kasar nan na kokarin kafa kungiya don hada kansu wuri daya da yin nazarin hanyoyin taimaka wa makarantarsu domin farfado da fannin ilimin da ya samu kansa cikin mawuyacin hali a wannan zamani.Tsofaffin daliban sun bayyana haka ne a Gidan Matasa, inda suka shirya wa daya […]

Tsofaffin daliban Kwalejin Makwa za su kafa kungiya don farfado da ilimi
Tsofaffin daliban Kwalejin Makwa za su kafa kungiya don farfado da ilimi

Tsofaffin daliban Kwalejin Makwa da ke sassa daban-daban na kasar nan na kokarin kafa kungiya don hada kansu wuri daya da yin nazarin hanyoyin taimaka wa makarantarsu domin farfado da fannin ilimin da ya samu kansa cikin mawuyacin hali a wannan zamani.
Tsofaffin daliban sun bayyana haka ne a Gidan Matasa, inda suka shirya wa daya daga cikinsu, wanda yake Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Alhaji Sa’idu Ndako Idris Kpaki liyafar taya shi murnar mukamin da aka nada shi.
Sun ce kafa kungiyar za ta ba su damar tuntubar juna akai-akai da nufin su rika haduwa suna tattauna muhimman al’amuran da suka shafi makarantar da bullo dabarun warware wasu daga cikin matsalolin da ke ci mata tuwo a kwarya.
Da yake jawabi,Tsohon Shugaban daliban Kwalejin  a shekarar 1978, Malam Aliyu Bagudu Bello, a hirarsa da Aminiya, ya ce sun sha taimaka wa kwalejin ta fuskoki da dama,ba a kungiyance ba, amma suke son su karfafa abin, a wannan lokacin.
Ya tabbatar cewar tsofaffin daliban za su yi amfani da matsayinsu da karfinsu da kuma aljuhunsu wajen tallafar makarantar tasu,musamman wajen gyara azuzuwa da gidajen kwanan dalibai.
Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Alhaji Sa’idu,ya bayyana liyafar da aka shirya masa babban kalubale a gare shi domin ya hada hancin abokansa cikin lokaci kankane su cigaba da gudanar da ayyukan da za su samar da yanayin da ya kamata don dalibai su rika daukan darussa yadda ya kamata.