Tsofaffin furodusoshin Kannywood da aka daina jin ɗuriyarsu

Aminu Mirror fitaccen furodusa ne a Zaria, wanda ya yi fice a shekarun 2000, sai dai an daina jin ɗuriyarsa tun rasuwar abokinsa Ahmed S. Nuhu.

Tsofaffin furodusoshin Kannywood da aka daina jin ɗuriyarsu

Masana’antar Kannywood ta dade tana nishaɗantar da al’umma, musamman Hausawa da sauran kabilun Arewacin Najeriya.

A makon jiya Aminiya ta ruwaito cewa kasuwancin fina-finan ya samu koma-baya matuƙa, wanda hakan ya sa wasu suke nuna yatsa ga furodusohin yanzu kan gaza shirya fim ɗin da za a iya haskawa a Netflix da sauran manyan hanyoyin nuna fina-finai da za su samar wa masana’antar kuɗin shiga.

Wannan ya sa Aminiya ta yi waiwayen wasu furodusohin da aka daina jin ɗuriyarsu a masana’antar.

Salisu Galadanchi – Shi ne Daraktan Fim din Turmin Danya, fim na farko a Kannywood, ya yi ritaya daga aikin gwamnati a Gidan Talabijin na CTV, yana zaune a Kano.

Umar Sheikh Mohammed: Shi ne mai Kamfanin Godiya and Dan Hassan wanda ya shirya fina-finan barkwanci, shi ma ya yi nukusani.

Bala Ahmed: Ana kiransa da Bala Sarauniya saboda rawar da ya taka wajen shiryawa da gabatar da finafinan Kamafanin Sarauniya Films a Kano.

Auwalu Mohammed Sabo shi ne Furodusan Kamfanin Sarauniya Films wanda suka yi finafinan gargajiya irin su Sangaya da Daskindaridi da Linzami da Wuta da sauransu. Yanzu yana aiki a Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Ali Jindos Aneesa: Tsohon mai daukar hoto na masana’antar, wanda ya koma shirya fim. Shi ya kawo Saratu Daso Kannywood a inda ya sa ta a fim din sa Feleke.

Habibu Sani: Tsohon mai shirya finafinai na Kamfanin K Films Multi Services, kuma tsohon ma’aikacin Hukumar Tarihi da Al’adun Gargajiya ta Jihar Kano, shi ne Furodusan Saki Reshe 2 da Reshe Ya Juye da Mujiya 1 da na 2. Shi ne kuma ya jagoaranci Kungiyar AHFIP a zamanin Abubakar Rabo.

Auwalu Isma’il Marshal: Tsohon Shugaban Kungiyar Tumbin Giwa da ta koma Tumbin Giwa Films, ya jagoranci shirin finafinai, yanzu kuma Shugaban Kungiyar Dattawan Kannywood.

Adamu Mohammed. Shi ne mai Kamfanin Kwabo Films, wanda ya yi fim din Kwabon Masoyi daga littafinsa mai wannan suna da kuma Dan Almajiri na 1 da na 2.

Umar Bawa Dukku: Shi ne mai Kamfanin Dukku Productions wanda ya shirya finafinan barkwannci da dama. Shi ne kuma wanda ya fara buga fim a faifan SIDI da fim din sa mai suna Zainab a lokacin ana sakin finafinai a kaset.

Hamisu Lamido Iyan Tama: Shi ne mai Kamfanin Iyan Tama Multimedia, finafinan Gashin Kuma da Kilu Ta Ja Bau, na daga cikin finafinan da kamfaminsa ya shirya, baya ga buga wakoki na sauran finafinai da kuma fito da Ali Baba Yakasai wanda ya fara buga wa Rarara kida.

Abubakar A. S. Mai Kwai: Shi ne mai Kamfanin Mai Kwai Mobies, inda ya shirya kuma ya dauki nauyin finafinai irinsu Kona Gari, Munafikin Mata da sauransu.

Abdullahi Maikano: Mazaunin garin Kaduna ne, ya yi suna a shirya finafinai a baya, ya taba zama Shugaba Kungiyar MOPPAN

Yakubu Lere: Fitaccen furodusa da ya yi fim din Wasila na 1 da na 2 a karkashin kamfaninsa na Lerawa Films da kuma wasu finafinan. Ya taba zama mai ba Gwamnan Jihar Kaduna Shawara kan Harkar Yada Labarai.

Aminu Hudu: Mai Kamfanin ALMAH Productions, tsohon furodusa ne da ke garin Jos ya yi suna a harkar sayar da kaset kafin ya koma shirin fim a shekarun 1990.

Rabi’u HRB: Shi ne mai Kamfanin HRB Films mai ofishi a Kano daga baya ya koma Kaduna. Ya yi finafinai da yawa a ciki har Gyale da kuma Abin Sirri Ne.

 Ibrahim Dahiru: Shi ne mai Kamfanin 3SP a Jos, ya yi finafinai da dama a karkashin kulawar Abubakar da kuma Shehu.

Bala Anas Babinlata: Koda yake an fi saninsa a harkar rubutu da kuma bayar da umarni, amma ya yi finafinai na kansa a karkashin kamfaninsa Babinlata Films Sarma-Sarma na daya daga cikinsu.

Hajiya A’isha Halilu: Tana daya daga cikin furudusoshi mata da ake ji da su a da.fim din Sahnafahna, daya daga cikin finafinanta da suka yi tashe a karkashin kamfaninta na Kumbo Productions.

Sani Mu’azu: Koda yake ya yi fice a shirye-shiryen talabijin inda yake fitowa a matsayin jarumi, Kamfaninsa na Lenscope Media da ke Jos ya kwanta dama a harkokin Kannywood. A baya sun yi finafinai da kuma samar da mawaka a masana’antar.

Alhaji Ibrahim Mandawari: Shi ne shugaban Kamfanin Mandawari Enterprises da ya shirya finafinai da dama irin su Zakaran Gwajin Dafi da Marainiya da Gaskiya Dokin Karfe.

Aminu Mirror: Aminu Mirror fitaccen furodusa ne a Zaria, wanda ya yi fice musamman a tsakanin 2000s, sai dai an dain jin ɗuriyarsa tun rasuwar abokinsa Ahmed S. Nuhu. Daga cikin finafinan da ya shira a Kamfanin Ijaba Productions akwai Ibro Police da Sirri ne.

Sai ya sake dawowa a fim din Gidan Badamasi mai dogon zango a matsayin Malam Zaidu.

Aminu Bizi: Shi ne Shugaban Kamfanin Bizi Productions, kuma ya shirya finafinai irinsu tsohon dan siyasa da Baba Ari ya ja da sauransu.

Ahmed Bifa: Shugaban Kamfanin Bifa Productions. Ya shirya finafinai irinsu Kyandir da Bakar fuska.