Tsofaffin Kansilolin Bauchi sun bukaci gwamnati ta biya su hakkokinsu
kungiyar Tsofaffin Kansiloli ta kasa reshen Jihar Bauchi ta bukaci agajin gaggawa daga hukumomin da ke da ruwa da tsaki don tilasta Gwamnatin Jihar Bauchi wajen biyan su hakkokinsu na albashi da alawus-alawus da suke bi a jihar tsawon shekaru. Alhaji Sama’ila Gumau ne ya yi wannan kira, a yayin da ya jagoranci tawagar kansilolin […]

kungiyar Tsofaffin Kansiloli ta kasa reshen Jihar Bauchi ta bukaci agajin gaggawa daga hukumomin da ke da ruwa da tsaki don tilasta Gwamnatin Jihar Bauchi wajen biyan su hakkokinsu na albashi da alawus-alawus da suke bi a jihar tsawon shekaru.
Alhaji Sama’ila Gumau ne ya yi wannan kira, a yayin da ya jagoranci tawagar kansilolin da ta kawo ziyara anan babban ofishinmu na Daily Trust dake Abuja a ranar Talatar da ta gabata.
Sama’ila Gumau ya ce kansilolin wadanda suka yi aiki tukuru don ci gaban al’ummarsu daga shekarar 2008 zuwa 2011 a yankuna daban-daban na jihar, sun biyo bashin albashi da sauran alawus-alawus da suka haura naira miliyan 500.
Har ila yau ya bayyana cewa, duk da daruruwan alkawura da gwamnatin jihar ta rika yi masu a lokuta daban-daban na cewa za ta biya kudaden, amma matsalar ta ci gaba har zuwa yau, ba tare da samun ko kwandala ba.
“Mun fara gabatar da wannan koken a gaban Babbar Kotun Sasanta Ma’aikatu ta kasa reshen Jos a Jihar Filato, inda kotun ta duba lamarin sannan ta bada umarnin cewa a gaggauta biyanmu dukkan hakkokinmu, sannan kuma ta tsaida asusun dake dauke da kudaden namu har sai an rattaba hannu kan takardar biyanmu. Amma a maimakon haka, sai gwamnatin ta hada kai da wasu bankunan da rufe asusun ya shafa su ka sake daukaka kara sun a kalubalantar wancan sakamakon, shari’ar da kenan ta ki ci ta ki cinyewa tsawon shekaru sannan a matsayinmu marasa karfi mun galabaita ainun,” in ji shi.
“A yanzu haka shari’ar ta na gaban Katun daukaka kara ta Jos, inda ake ci gaba da tsawaita shari’ar da gangan. A yayin da kuma iyalanmu ke cikin wani hali na rayuwa, domin mafi yawanmu ba mu iya daukar nauyinsu da ya rataya akanmu. Kai ba mu san ma makomar mu ba a halin yanzu duk da cewa tare da mu aka kafa wannan gwamnatin ta Bauchi. Don haka mu na kira ga Babban Jojin Najeriya da Shugabar Katun daukaka kara ta Tarayya da Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai ta Tarayya su shiga wannan magana don kwato mana hakkinmu daga wannan zaluncin,” Alhaji Sama’ila Gumau ya bukata.