Tsofaffin kasar Sin na kashe kansu don kada a hana su shiga makara – rahoto
Gwamnatin garin Anking da ke Gabashin birnin Anhui, sun bayar da umarnin duk wanda ya mutu jibi Lahadi, daya ga watan Yuni, za a kone gawarsa, kamar yadda Jaridar Beijing News Daily ta ruwaito, don haka tsofaffi ke ta halaka kansu, don gudun kada a hana musu shiga makara.Tsofaffi shida ne suka yi wa Kansu […]
Gwamnatin garin Anking da ke Gabashin birnin Anhui, sun bayar da umarnin duk wanda ya mutu jibi Lahadi, daya ga watan Yuni, za a kone gawarsa, kamar yadda Jaridar Beijing News Daily ta ruwaito, don haka tsofaffi ke ta halaka kansu, don gudun kada a hana musu shiga makara.
Tsofaffi shida ne suka yi wa Kansu kisan gilla, don tabbatar da cewa sun mutu kafin sabuwar dokar hana amfani da makara wajen binne mamaci tafara aiki, kamar yadda jaridar ta ruwaito.
kasar Sin tana da daddiyar al’adar bauta wa magabata, al’amarin da ya tanadi iyalai su binne danginsu, su yi musu tulluwa a kan kaburburansu.
Wata tsohuwa ’yar shekara 91, mai suna Wu Zhengde, ta rataye kanta, tun a ranar 5 ga Mayu, bayan da ta samu labarin sabuwar dokar. Sai kuma wata matar mai suna Zheng Shifang, ’yar shekara 83, ta kashe kanta, bayan da jami’an hukuma suka fasa mata makararta gida biyu.
Wata ’yar shekara 68 ta halaka kanta ne ta hanyar aukawa rijiya, yayijn da wasu ke shan guba.
Duk da wadannan al’amuran kisan gillan kai da ke aukuwa, jami’an hukuma sun ce, yawan halaka kai ba shi da nasaba da hana binne mutane, kuma mutane da kansu suke mika makararsu.
“kasar Sin na da girma, mutuwa da rashin lafiya a tsakanin tsofaffi al’amari ne da aka saba da shí,” kamar yadda rahotanni suka bayyana daga jami’an karamar hukuma.
Jaridar ta tuntubi wani lauya a birnin Beijing, Zheng Daoli, wanda ya bayyana cewa kwace makarar da ake yi ya saba wa doka, saboda makarar dukiya ce ga masu ita.
A wasu sassa na kasar Sin kuwa, jami’an kananan hukumomi suna ta kokarin shawo kan al’umma, sun amince su “baje kaburbura,” don a samu isasshiyar kasar noma da aiwatar da ayyukan raya kasa.
Jami’an hukuma a tsakiyar gundumar Henan, sun baje kaburbura har dubu 400 tun a shekarar 2012, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bayyana.
Mazauna yankunan karkara da ke garin Ankying, sun samu labarin dokar ne a cikin watan Afrilun bana, bayan da suka shafe shekara 10 suna shirya makarar da za a binne su.
Wata ’yar kauye ta bayyana cewa: “Na yi matukar san wahala a rayuwa, don haka nike son in kwanta inda zan samu kariya daga ruwan sama, a cikin makara.”