Tsofaffin ma’aikatan Bankin Arewa sun yi barazanar rufe rassan Bankin Unity
Tsofaffin ma’aikatan rusasshen Bankin Arewa (Bank of the North) da yanzu ya narke a Bankin Unity da ke bankin bashin kudin fansho na fiye da shekara tara sun yi barazanar rufe rassan bankin Unity nan da mako biyu idan ba a biya su hakkokinsu ba.Tsohon shugaban ma’aikatan bankin Kwamared Babayola Muhammad Isah ne ya bayyana […]

Tsofaffin ma’aikatan rusasshen Bankin Arewa (Bank of the North) da yanzu ya narke a Bankin Unity da ke bankin bashin kudin fansho na fiye da shekara tara sun yi barazanar rufe rassan bankin Unity nan da mako biyu idan ba a biya su hakkokinsu ba.
Tsohon shugaban ma’aikatan bankin Kwamared Babayola Muhammad Isah ne ya bayyana haka a lokacin da ya gudanar da taron manema labarai a Cibiyar ’Yan jarida ta jihar da ke Gombe
Ya ce tuni Babban Bankin Najeriya ya umarci bankunan kasar nan su biya tsofaffin ma’aikatansu hakkokinsu kafin su hade da kowane banki, amma Bankin Unity ya yi biris da wannan umarni.
Ya ce wani lokaci a shekara ta 2006 bayan sun yi jira na tsawon shekara biyu, bankin na Unity ya biya kashi hamsin ne kawai cikin dari na fansho da giratutinsu.
Kwamared Babayola, ya cewa rashin biyansu hakkokinsu ya jefa su cikin halin ni’yasu, har wasu suka mace. Ya ce kudaden nasu ne bankin yake ta juyawa a matsayin riba amma su masu hakkin suna mutuwa da yunwa saboda hana su hakkokinsu. Ya ce Naira biliyan biyar da miliyan 665 na hakkokinsu da ya kamata a biyasu ne bankin ke tinkahon cewa ribar da ya samu a shekarar 2010.
Ya ce hatta gwamnonin Arewa da suke da ruwa da tsaki a harkar bankin sun sa baki a wani taro da suka gudanar a Kaduna domin a biya su hakkokinsu amma saboda son rai sai bankin ya yi watsi da batun ya ki amincewa ya biya su.
Ya ce sun gama shirin kulle rassan bankin Unity a fadin kasar nan, bayan sun ba bankin wa’adin mako biyu daga 18 ga Yuni zuwa 5 ga Yulin bana, don a biya su sauran fansho dinsu, ko kuma su fara rufe rassan bankin Unity daga ranar 8 ga Yuli mai zuwa a Legas da Abuja da Kano da sauran jihohi.