Tsofaffin ma’aikatan Gombe 2,204 sun karɓi giratuti N4.2bn

Gwamnan ya yi alƙawarin cews kafin wa’adinsa ya ƙare zai biya sauran ma’aikata haƙƙinsa.

Tsofaffin ma’aikatan Gombe 2,204 sun karɓi giratuti N4.2bn

Gwamnatin Jihar Gombe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ta biya tsofaffin ma’aikata 2,204 kuɗaɗen giratuti na Naira biliyan 4.2.

Wannan na cikin wani yunƙuri na rage basussukan da gwamnan ya gada daga gwamnatin da ta gabace shi.

Majalisar zartarwar jihar ce, ta amince da biyan kuɗaɗen a makon da ya gabata, wanda ya shafi ma’aikatan da suka yi ritaya tsakanin 2019 zuwa 2020.

Gwamnan, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta riga ta biya jimillar Naira biliyan 17.2 daga cikin bashin Naira biliyan 21 da ta gada.

Ya kuma alƙawarin cewa sauran za a kammala biya kafin ƙarshen wa’adin mulkinsa.

“Kafin shekarar 2027, za mu tabbatar da cewa dukkanin tsofaffin ma’aikata sun samu hakkokinsu yadda ya kamata,” in ji gwamnan.

Ya kuma ƙara da cewa tuni aka biya tsofaffin ma’aikata 11,685, da suka yi ritaya tsakanin shekarar 2014 zuwa 2018, jimillar Naira biliyan 13.

Ya ce sabon biyan na yanzu ya shafi waɗanda suka yi ritaya tsakanin 2019 zuwa 2020.

Dangane da tsofaffin ma’aikatan ƙananan hukumomi, gwamnan ya ce an tsara dabarun biyan kuɗaɗensu dangane da ƙarfin kowace ƙaramar hukuma.

Ya ce hakan zai wakana ne tare da haɗin guiwar shugabannin ƙananan hukumomin domin faɗaɗa wannan tsari zuwa gare su.

Gwamnan ya kuma jaddada wasu ƙarin gyare-gyare da gwamnatinsa ta yi wa ma’aikata, ciki har da ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa Naira dubu 70.

Ya ƙara da cewar gwamnatin ta kafa Hukumar Gyaran Ma’aikata, da kuma amfani da fasahar zamani wajen tantance ma’aikata domin tabbatar da gaskiya.

Shugaban Ƙungiyar Tsofaffin Ma’aikata ta Jihar Gombe (NUP), Barista Aliyu Gadalima Doho, ya yaba wa wannan matakin.

Ya bayyana biyan kuɗaɗen giratutin a matsayin abin da “ya ceci rayuwar” tsofaffin ma’aikata da iyalansu.

Shi ma shugaban kwamitin biyan kuɗaɗen, Muhammad Buba, wanda shi ne babban mai binciken kuɗin jihar, ya jinjina wa gwamnan bisa fifita biyan haƙƙoƙin ma’aikata.