Tsofaffin ma’aikatan tashoshin jiragin ruwa sun nemi a biya su fansho na shekara 10

Tsofaffin ma’aikatan tashoshin jiragen ruwan Najeriya sun yi kwarya-kwaryar zanga-zangar lumanaa gaban ofishin Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa da ke Legas, dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce da daban-daban,  da wasu ke cewa “Yau shekara 10 da kuka dakatar da mu amma a biya mu hakkinmu abu ya gagara.”Ma’aikatan sun ce abin da ke ba su mamaki […]

Tsofaffin ma’aikatan tashoshin jiragin ruwa sun nemi a biya su fansho na shekara 10
Tsofaffin ma’aikatan tashoshin jiragin ruwa sun nemi a biya su fansho na shekara 10

Tsofaffin ma’aikatan tashoshin jiragen ruwan Najeriya sun yi kwarya-kwaryar zanga-zangar lumanaa gaban ofishin Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa da ke Legas, dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce da daban-daban,  da wasu ke cewa “Yau shekara 10 da kuka dakatar da mu amma a biya mu hakkinmu abu ya gagara.”
Ma’aikatan sun ce abin da ke ba su mamaki shi ne sun jiyo daga majiya mai tushe cewa a biya su wadannan kudade amma da suka zo wurin hukumar sai ta ce ba ta san da wannan magana ba.
daya daga cikin tsofaffin ma’aikatan mai suna Alhaji Yusuf ya ce zanga-zangar ba tashin hankali ba ce illa ta neman hakkinsu.
Ya ce abin da ke ba su mamaki shi ne yadda ma’aikatan tashoshin jiragen ruwa da ya kamata su tausaya musu domin a biya su hakkinsu saboda su ma wata rana za su samu kansu a irin matsayinsu amma ba su yin haka.
Wani mai suna PC Kayinem ya ce ba za su bar zuwa gaban harabar hukumar domin yin zanga-zangar lumana ba har sai hukumar ta saurare su.
Lokacin da Aminiya ta tuntubi Shugaban Hukumar Alhaji Habibu Abdullahi game da zargin ba a biya tsofaffin ma’aikatan hukumar fansho na tsawon shekara 10 ba, ya ce wannan batu ba gaskiya ba ne. Ya ce gaskiyar maganar ita ce hukumar tana da ma’aikata dubu 13, kuma da aka zo ana son a bayar da hukumar haya ga ’yan kasuwa sai gwamnati ta ce, ta yaya za a rage ma’aikata ba tare da wadanda za a rage sun ji radadin haka ba.
Ya ce a yunkurin dadada wa wadanda za a rage ne aka cimma matsayar cewa duk wanda zai tafi za a   ba shi albashinsa na shekara biyar a dunkule domin ya samu jarin tsayawa kan kafafunsa.
Alhaji Habibu ya ce ba a cimma wannan matsaya ba sai da kungiyar Kwadago reshen hukumar da Hukumar Jin Dadin Ma’aikata ta kasa da su ma’aikatan suka sa hannu sannan aka biya kowannensu albashin shekara biyar a matsayi kudin sallama.
Ya ce sai yanzu kwatsam bayan an dauki lokaci mai tsawo suka tayar da kayar baya wai a biya su fansho na shekarun.
Alhaji Habibu ya ce bai san inda suka samo bayanin kan a biya su kudaden da suka ci suna bi ba, domin kudin hayar da hukumar ta amsa ta mika wa Gwamnatin Tarayya ce, kuma zuwa lokacin da yake magana gwamnatin ba ta aiko wa hukumar da wata takardar umarnin a biya tsofaffin ma’aikatan fansho na shekarun da suka fada ba.