Tsoffin Gwamnonin Da Ke Dumama Kujera A Majalisar Dattawa
Kowannensu ya shekara takwas a matsayin gwamnan jiharsa kafin daga bisani ya lashe zaben zuwa Majalisar Dattawa domin wakiltar al’ummarsa
Wani kundi da muka yi karo da shi ranar Lahadi ya nuna cewa hudu daga cikin tsoffin gwamnonin Najeriya 13 da ke Majalisar Dattawa a yanzu sun kwashe watanni 10 ba tare da sun mika kudiri ko daya ba.
Kafin su ci zaben da ya kawo su Majalisar Dattawan, tun da farko sai da kowanne daga cikin tsoffin gwamnonin hudu ya kwashe shekaru takwas a yana shugabancin al’ummar jiharsa.
Daga cikinsu, tsohon dan gwagwarmaya kuma tsohon shugaba kungiyar kwadago ta kasa (NLC), tsohon Gwamnan Jihar Edo Adams Oshiomole, ya shafe watanni 10 bai mika wata bukatar jama’arsa ga majalisar ba.
Haka kuma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Sanata Abdulaziz Yari, babu kudirin da ya gabatar a watanni 10 da ya shafe a majalisar zuwa yanzu.
- NAJERIYA A YAU: Wa Ke Da Ikon Dakatar Da Ganduje A Jam’iyar APC?
- Har yanzu Gwamnatin Tarayya na biyan tallafin man fetur — El-Rufai
Na uku shi ne tsohon Gwamnan Bayelsa, Serieke Disckson, wanda kundin ya tabbatar mana cewa shi ma bai mika wata bukatar jama’arsa ga majalisar dattawan ba.
Sunan tsohon Gwamnan Jihar Filato Simon Bako Lalong, ya bayyana a cikin kundin a matsain tsohon gwamna na hudu da bai mika kuduri ba, duk da cewa Sanata Lalong bai kai sauran takwarorin nasa jimawa a zauren ba.
Sanata Lalong dai ya yi aiki a matsayin Ministan Kwadago da Ayyuka a farkon Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Daga bisani kotu ta tabbatar da nasarar zabensa a matsayin Sanatan Filato ta Kudu, inda ya shiga zauren Majalisar Dattawan a watan Disamba 2023, kimanin watani hudu da suka gabata.
Majalisar Dattawa ita ce babbar zauren bangaren kafa dokokin Najeriya, inda zababbun wakilai daga mazabu 109 da ke kasar ke tattaunawa muhimman batutuwa da kuma kafa dokoki domin kyautata rayuwar ’yan kasar.
Wani mai sharhi a kan kimiyyar siyasa, Aminu Yakudima, ya bukaci wadannan tsoffin gwamnoni su farka da barcin da suke yi su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
Aminu Yakudima ya ce, ana sa ran tsoffin gwamnoni su zo majalisa da kwarewa da gogewa da sanin bukatun jama’arsu.
Don haka ana tunanin sun san makamar aiki, za su zo da kudurori masu inganci domin kawo cigaba mai dorewa a kasa.
“Zai zamo abin mamaki a ce wadannan tsoffin gwamnonin za su zamo masu dumama kujerun zauren majalisa, inda ake zaton za su ba da gudunmawa wurin kawo cigaba.
“Dole ne a ba su shawara su mike tsaye su zage damtse domin taimaka wa kasar nan da kwarewar da suka samu.”
Jackson Lekan Ojo shi ma dai cewa ya yi “ya zama wajibi tsoffin gwamnonin su sauke nauyin da suka dauka muddin suna so su zamo masu fada a ji.
“A bayyane yake cewa sun nemi tahowa zauren Majalisar Dattawa ne domin su ci gaba da zama masu fada a ji a yankunansi da ƙasar ma baki daya, don haka ya zama wajibi su daure su yi abin da ya dace domin samar da ingantaccen wakilci.”
Da yake martani kan batun, Sanata Oshiomole ya ce kudurinsa ya kusa isowa.
Simon Makut mataimaki na musamman ga Sanata Lalong, a sakon tes kwana, ya ce “Sanata Lalong zai mika kudiri”.
Duk kwakwarmu wurin jin ta bakin Sanata Yari da Dickson abin ya ci tura.
Ba su amsa wayoyinsu ba, kuma ba su ce uffan ga sakonnin tes da na WhatsApp da muka aika musu ba.