Tsoffin ’yan Boko Haram sun yi bore a Borno
Daruruwan tubabbun ’yan Boko Haram a Jihar Borno sun tayar da tarzoma kan rashin biyan su alawus din da gwamnati ta yi musu alkawari.
Daruruwan tsoffin mayaƙan Boko Haram da ke tsare a sansanin Hajji da ke Jihar Borno bayan da suka miƙa wuya sun tayar da tarzoma kan rashin biyan su alawus na Naira 30,000 da gwamnati ta yi alkawari.
Tsoffin mayaƙan sun tare babbar hanyar Bulumkutu zuwa Maiduguri a ranar Juma’a, lamarin da ya sa mazauna fargaba, da kuma cunkoson ababen hawa.
- Nijar ta fara ɗaukar sojojin sa-kai, Mali da Burkina Faso sun ba ta jiragen yaƙi
- ’Yan bindiga sun harbe mai fafutikar kare hakkin bakar fata a Brazil
Da yake tsokaci kan hakan, Farfesa Usman Tar, Kwamishinan Yada Labarai da Tsaro na Cikin Gidan Jihar, ya ce tantance adadin tubabbun masu tayar da kayar baya ne ya haifar da hakan.
Ya ce bayan dawowar zaman lafiya, jami’an gwamnatin jihar a ranar Juma’a sun dawo aikin tantance tubabbun mayakan Boko Haram, wanda a baya aka dakatar.
A cewarsa, “ya zuwa yanzu adadin tubabbun ’yan tada kayar baya ya kai 6,900 a karkashin tsarin hukumomi da yawa na kwance damarar tsoffin mayaƙan Boko Haram a ƙarƙashin shirin da ake cewa, “Model Borno.”
“Koyaya lamarin yake dai an samu matsala ne ta sadarwa waɗanda ya kamata su bayyana don ɗaukar bayanan shi ne aka samu ’yar matsala wanda hakan ya haifar da rudani a sansanin da ake gudanar da wannan aiki na tantancewa wadda aka kasa shi gida shida.
“Gwamnatin Jihar Borno na son tabbatar wa jama’a cewa an shawo kan lamarin kuma an dawo da zaman lafiya a wurin da ake gudanar da tantancewar da na’urar tantancewa don ajiye bayanan kowannensu,” inji shi.
Wannan aiki dai wani muhimmin aiki ne da hukumomi ke fuskanta na sake shigar da tsoffin mayaƙa cikin al’ummomin da suka sha fama da hare-hare da garkuwa da su na tsawon shekaru 13 da sunan jihadi.