Tsoho a Sin ya ki yin aure don kula da marayu
Tun a shekarar 1954, a kasar Sin Peng Yunsong ya fara rainon maraya an shekara takwas, mai suna Yan Jingcheng; kuma tsawon shekara 15 sai Peng ya auki wasu marayu har guda biyar. Duk da cewa, marayun da Peng ke riko sun fito daga iyaye daban-daban, ya mayar da su tamkar ‘’ya’yan mutum guda da […]
Tun a shekarar 1954, a kasar Sin Peng Yunsong ya fara rainon maraya an shekara takwas, mai suna Yan Jingcheng; kuma tsawon shekara 15 sai Peng ya auki wasu marayu har guda biyar. Duk da cewa, marayun da Peng ke riko sun fito daga iyaye daban-daban, ya mayar da su tamkar ‘’ya’yan mutum guda da suka fito daga zuri’a guda.
Wkannan ’ya’yan riko na Peng sun haa da Yan Jingcheng da Guo Tingzhong da Zhang iuking da Gao Yubin da Luan Jingtong, da Liu Yuzheng.
Peng dai bai taba yin aure ba. Shi ma’aikaci ne a wata masana’anta, inda yake kwasar shara a kan hanya, sannan yana yin wasu ’yan aikace-aikace don ya samu kuin tallafar rayuwar ’ya’yansa. Yanzu Peng na da shekara 97, kuma wannan hidima da ya aikata ta bijiro masa da alheri. Domin aukacin ’ya’yan riko shida da ya raine su, sun samu kyakkyawar rayuwa.
Duk da cewa rayuwar marayun Peng ta yi kyau, ya ki yarda ya zama nauyi a gare su. Domin sai a shekarar 2013, bayan ya cika shekara 94, sannan ya amince ya koma garin Harbin kusa da aya daga cikin marayun da ya raina, mai suna Luan Jingtong. Kai har a ’yan kwanakin nan Peng yana aikin karfi na sa’o’i huu a kowace rana a wani gidan saukar baki. Kuma a lokutan da ba ya aikin komai, yakan yi amfani da shafin sadarwa na WeChat ya tattauna da’ya’yansa da jikokin sa.