Tsoho mai shekara 63 ya rataye kansa a Sakkwato

Wani tsoho dan shekara 63 mai suna Malam Iliya Shehu da ke zaune a unguwar Tudun wada a cikin babban birnin jihar Sakkwato ya rataye kansa. Malam Iliya ya rataye kansa a cikin gidansa da misalin karfe biyu na rana, a ranar Litinin da ta gabata.Abinciken da Aminiya ta yi, wata majiya ta sheda mata […]

Tsoho mai shekara 63 ya rataye kansa a Sakkwato
Tsoho mai shekara 63 ya rataye kansa a Sakkwato

Wani tsoho dan shekara 63 mai suna Malam Iliya Shehu da ke zaune a unguwar Tudun wada a cikin babban birnin jihar Sakkwato ya rataye kansa. Malam Iliya ya rataye kansa a cikin gidansa da misalin karfe biyu na rana, a ranar Litinin da ta gabata.
Abinciken da Aminiya ta yi, wata majiya ta sheda mata cewa tsohon ya rataye kansa ne a dalilin rashin haihuwa da bai samu ba: “ina ganin bakin cikin rashin  haihuwa ne ya kai shi ga yin haka’ a cewar majiyar.”
Malam Ladan Shehu kani ne ga margayin kuma makawabtan juna ne, a zantawar da aka yi da shi cewa ya yi, “Yayana dan shekara 63 yana fama da rashin lafiyar kwakwalwa, waton tabin hankali, tsawon shekara 40,ya rabu da matarsa tun da dadewa a kulum gidana ake bashi abinci, baya da kowace matsala ban da wannan. Kuma yana da tacewa ga diyanmu da jikokinmu kai ka ce shi ya haife su da kansa, ni na san ba ya tare da bakin cikin rashin haihuwa ko na matarsa,don ba haka ba gaskiya ba ne kamar yadda ake fadin rashin haihuwa ne ya kai shi ga halaka kansa. A zatona rashin lafiyarshi ne yakai shi ga yiwa kansa haka.”in ji shi
Malam Ladan ya kara da cewa “Da misalin karfe biyu na rana a jiya ne(Litinin)na same shi cikin gidansa ya rataye kansa sai ban taba shi ba,na yi sauri na je ofishin ‘yansanda na Unguwar Rogo na gaya musu suka zo muka tafi asibitin kwararru ta jiha likita ya  tabbatar da shi ne ya rataye kansa da kansa, daga nan aka ba mu shi muka yi masa sutura irin ta addinin musulunci.”
DSP El-mustafa Sani jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Sakkwato ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce suna kara gudanar da bincike kan lamarin.