Tsoho mai shekara 75 ya shiga hannu kan zargin damfara

Wani tsoho mai shekara 75 mai suna Alhaji Ali Yahaya Ringim da ke zaune a Tudun Wadan Kaduna ya shiga hannun jami’an tsaro na sibil difens kan zarginsa da karbar Naira miliyan daya da dubu 215 daga hannun dalibai da sunan zai nema musu aiki. An kama tsoho ne a garin Ringim, kuma ana zargin […]

Tsoho mai shekara 75 ya shiga hannu kan zargin damfara
Tsoho mai shekara 75 ya shiga hannu kan zargin damfara

Wani tsoho mai shekara 75 mai suna Alhaji Ali Yahaya Ringim da ke zaune a Tudun Wadan Kaduna ya shiga hannun jami’an tsaro na sibil difens kan zarginsa da karbar Naira miliyan daya da dubu 215 daga hannun dalibai da sunan zai nema musu aiki.
An kama tsoho ne a garin Ringim, kuma ana zargin ya hada baki ne da wani tsohon dan sanda mai suna Adamu Hassan wanda surukinsa ne da ke bayyana kansa da jami’in hukumar cika-aiki da ke Abuja wajen yin wannan damfara.
Asirin tsohon ya tonu ne lokacin da ya je ta’aziyya bayan shekara biyu da amsar kudin masu neman aikin amma ba amo ba labari, inda matasan na ganinsa suka sanar da jami’an sibil difens suka kama shi.
Wani matashi mai suna Abubakar Mu’awiyya ya ce su 27ne tsohon ya amshi Naira dubu 45 daga kowannesu da sunan za a ba su aiki amma shekara biyu babu labari kuma ya dauke kafarsa daga zuwa Ringim sai yanzu da ya zo ta’aziyyar wani dan uwansa da ya rasu.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai a hedkwatar sibil difens da ke Dutse, Ali Ringim ya yi nadamar halin da ya samu kansa a ciki, ya ce ogansa wanda kuma surukinsa ne, bai yi tsammanin macuci ba ne amma an wayi gari ya jefa shi cikin halin damuwa
Ya ce ya dauka takardun daukar aiki da surukinsa ya ba matasan 27 masu kyau ne ba jabu ba kamar yadda matasan suke fada. Alhaji Ali ya ce bai san damfara ya yi wa matasan ba domin a cikin wadanda aka damfaradin harda jikansa