Tsoho mai shekara 84 ya kashe matarsa saboda ba ta yarda ya sadu da ita

Ya kuma yi zargin tana saduwa da wasu mazan a waje

Tsoho mai shekara 84 ya kashe matarsa saboda ba ta yarda ya sadu da ita

Ma’aurata

’Yan sanda a Jihar Edo sun kama wani tsoho mai shekara 84 bisa zargin kashe matarsa mai shekara 74, saboda ta ki yarda ya sadu da ita.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar ce ta sanar da kama tsohon yayin wani bajekolin mutum 198 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a Jihar.

A cewar Kakakin rundunar a Jihar, Chidi Nwabuzor, an kama tsohon mai suna Gabriel Uhuwa ne bisa zargin kashe matarsa mai shekara 75, saboda ta ki amincewa ya sadu da ita a duk lokacin da ya bukata.

Kakakin ya ce a ’yan kwanakin nan dai tsohon ya sha samun matsala da matar tasa a kan hakkinsa na aure.

Sai dai ya ce har yanzu tsohon ko nadamar abin da ya aikata bai yi ba, inda ma yake cewa a yanzu ya yi maganin matsalar da ta dame shi.

Da yake jawabi ga ’yan jarida, tsohon ya ce, “Sam matata ba ta sauraro na. Duk lokacin da na bukaci ta zo mu kwanta, sai ta ki. Mun haifi ’ya’ya bakwai tare da ita; maza bakwai da mata biyu.

“Sai da na kai kararta ga ’yan uwana da ’yan uwanta, amma ta ki sauraro na, sannan kuma na rika jin wasu zantukan cewa wasu malaman coci na kwanciya da ita.

“Duk lokacin da na bukaci saduwa da ita, sai ta ce min ba ta lafiya, tana da cutar Olsa, amma kuma ina jin tana saduwa da wasu mazan. Ni kuma ba ni da kudin da zan iya neman karuwai.”

Ya ce bayan ya yi korafi, sai ’ya’yansa suka daina aiko masa da kudi, sannan suka daina daga wayarsa, inda ya ce matar tasa ce ta hure musu kunne.

“A ranar Asabar din makon da ya gabata, da rana a cikin gidanmu, sai na dauki adda na daddatsa ta. Na yi hakan ne cikin fushi saboda na huce takaici kuma duniya ta san halin da nake ciki,” in ji tsohon.

Sai dai ya ce daga bisani ya yi da-na-sanin kashe ta a kan aikata laifin.