Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Lawal Uwais ya rasu

Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Mohammed Lawal Uwais ya rasu yana da shekaru 89 a duniya.

Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Lawal Uwais ya rasu

Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Mohammed Lawal Uwais ya rasu yana da shekaru 89 a duniya.

Mmarigayin, wanda ya kasance Alkalin Alkalan na tsawon shekaru 11 daga 1995 zuwa 2006 ya rasu ne a Abuja ranar Juma’a.

Wata majiya daga iyalan mamacin ta tabbatar da rasuwar sannan ta ce shirye-shirye sun kankama na yi wa mamacin jana’iza.

An dai haifi marigayin ne a ranar 12 ga watan Yunin 1936 a Zariyan jihar Kaduna.

A zamanin da yake shugabancin Alkalan, ya kawo sauye-sauyen shari’a da dama musamman a bangaren fadada harkokin siyasa, inda hakan ya zama silar yi wa jam’iyyu da dama rajista a Najeriya.

Kazalika a shekara ta 2007, kuma jagoranci kwamitin yi wa harkokin zaben Najeriya kwaskwarima wanda tsohon Shugaban Kasa, marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa ya naɗa shi.