Tsohon Babban Hafsan Tsaro Ibrahim Ogohi ya rasu

Ya kasance sojan ruwa na farko da ya samu anini huɗu a aikin soja a mulkin farar hula.

Tsohon Babban Hafsan Tsaro Ibrahim Ogohi ya rasu

Tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Admiral Ibrahim Ogohi ya riga mu gidan gaskiya a safiyar wannan Lahadin.

Wata majiya daga iyalan marigayin ta ce tsohon hafsan tsaron ya rasu ne a asibiti sakamakon jinya da ya yi fama da ita.

Admiral Ibrahim Ogohi CFR FSS MSS PSC, wanda aka haifa a ranar 14 ga watan Nuwamban 1948 ya riga mu gidan gaskiya bayan shafe shekaru 75 a doron ƙasa.

Shi ne sojan ruwa na farko da ya fara zama Babban Hafsan Tsaron Nijeriya daga 1999 zuwa 2003 kuma sojan ruwa na farko da ya samu anini huɗu a aikin soja a mulkin farar hula.

Marigayi Admiral Ibrahim Ogohi ya kasance kwamandan jirgin Rundunar Sojin Ruwa na Eken NNS France a 1982, kwamanda NNS Anansa a 1985 kuma darakta a makarantar horas da dakarun soji ta NDA daga 1986 zuwa 1987.

An dai haifi marigayi Ogohi a garin Okura-Lafiya da ke Ƙaramar Hukumar Dekina a Jihar Kogi.