Tsohon Babban Jojin Bauchi ya rasu

Allah Ya yi rasuwa ga tsohon Babban Jojin Jihar Bauchi Mai shari’a Sabo Suleiman Darazo. Mai shari’a Sabo Suleiman Darazo wanda shi ne Barayan Darazo da ke Jihar Bauchi ya rasu yana da shekara 69.Ya rasu a gidansa da ke Unguwar GRA a garin Bauchi, kuma a shekara ta 2011 ne ya yi ritaya daga […]

Tsohon Babban Jojin Bauchi ya rasu
Tsohon Babban Jojin Bauchi ya rasu

Allah Ya yi rasuwa ga tsohon Babban Jojin Jihar Bauchi Mai shari’a Sabo Suleiman Darazo.

Mai shari’a Sabo Suleiman Darazo wanda shi ne Barayan Darazo da ke Jihar Bauchi ya rasu yana da shekara 69.
Ya rasu a gidansa da ke Unguwar GRA a garin Bauchi, kuma a shekara ta 2011 ne ya yi ritaya daga aikin gwamnati.
Ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya 14 da jikoki da dama, inda aka yi jana’izarsa a kofar fadar Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rulwanu Suleiman Adamu.