Tsohon dalibi ya kona ofishin shugaban jami’ar da ta hana shi digirinsa shekara 11
Tsohon dalibin zane-zane a jami’arr Maharaja Sayajirao, wanda ya kasance “jigon tashintashina a shekarar 2007,” ana zarginsa da kona ofishin shugaban jami’ar, saboda tsananin takaicin yadda aka dauki dogon lokacin kusan shekara 11 ba a ba shi digirinsa ba, a cewar ’yan sanda. A cewar Insefta haresh bora na ofishin ’yan sanda da ke Sayajigunj […]
Tsohon dalibin zane-zane a jami’arr Maharaja Sayajirao, wanda ya kasance “jigon tashintashina a shekarar 2007,” ana zarginsa da kona ofishin shugaban jami’ar, saboda tsananin takaicin yadda aka dauki dogon lokacin kusan shekara 11 ba a ba shi digirinsa ba, a cewar ’yan sanda.
A cewar Insefta haresh bora na ofishin ’yan sanda da ke Sayajigunj a Jihar Gujarat ta kkasar Indiya, Chandra Mohan, wand ayakasance dalibin tsangayar zane-zane a jami’ar tsawon shekara 11 yana tsare.
Jigar Inamdar , wani babban jigo a shugabannin jami’ar ta MSU ya ssamu raunuka lokacin da yake kokarin fitar da wasu kundayen bayanai bayan da wutar ta tashi da marece, a cewar ’yan sandan.
Mista Mohan, dan asalin gundumar Warangal da ke Telangana, ya yi kokarin ganin Shugaban jami’ar Parimal byas don ya ji dalilin da ya sanya aka dade da ba a ba shi shaidar karatun digirinsa ba Domin ya kammala karatun jami’ar tun a Mayun shekarar 2007.
Ya yi ikirarin cewa duk da rubuta dimbin wasiku ga hukumomin jami’ar bai samu amsa daga gare su ba.
A cewar ’yan sanda,Mista Mohan ya zo da kwalbar fetur bayan sun yi zazzafan cece-ku ce da Jaikumar Nair, wani mataimaki ga Mista byas kan ganawarsa da shugaban jami’ar, sai ya bulbule fetur din a shimfidar ofishin ya kunna wuta.
dakuna biyu da suka hada da ofishin shugaban jami’ar wuta ta cinye su kurrmus. Wasu kundayen bayanai sun yi fata-fata, don a cewarsu shugaban jami’ar baya ofishin lokacin da al’amarin ya faru.
’Yan sanda sun ce Mista Mohan ya yi ikrarin aikata laifin.
Mista Mohan ya taba kasance mutumin da aka tafka rikici kan aikinsa na karshe wajen kammala karatun digirinsa a jami’ar cikin shekarar 2007. An ruwaito yadda ya zana abin bautar addinin Hindu cikin mummunan yana yi, al’amarin da ya har zuwa mabiya addini a wajen ibadarsu na bishwa Hindu Parishad.
An baje kolin zanensa a wani shiri da aka gudanar a wannan jami’a mai shekara 69 da kafuwa, hatr ta kai ga an shiga takaddama da cece-ku ce kan ’yancin bayyana ra’ayi ta hanyar zayyana da zane-zane.
Kwamishinan ’yan sanda Manoj Shashidhar ya ce Mista Mohan Police zai gurfana a gaban kot, inda ’yan snda za a su bukaci a tsare shi kafin a yi masa shari’a.