Tsohon dan kwallon Chelsea Adrian Mutu ya nemi a ba shi jariri
Adrian Mutu, tsohon dan kwallon kulob din Chelsea da ke Ingila a ranar Talata da ta wuce ne ya nemi hukumomin kasar Sin su mika masa jaririn da wata mata ta jefar inda aka ceto shi daga bututun kashi ba tare da ya mutu ba.Hasalima dai tuni aka mika jaririn ga kakanninsa don cigaba da […]

Adrian Mutu, tsohon dan kwallon kulob din Chelsea da ke Ingila a ranar Talata da ta wuce ne ya nemi hukumomin kasar Sin su mika masa jaririn da wata mata ta jefar inda aka ceto shi daga bututun kashi ba tare da ya mutu ba.
Hasalima dai tuni aka mika jaririn ga kakanninsa don cigaba da kula da shi bayan da likitoci suka gudanar da gwaje-gwaje don tabbatar da lafiyarsa.
Daga baya mahaifiyar jaririn ta bayyana amma saboda zazzabin da take fama da shi inda aka kwantar da ita a asibiti, tuni hukumomin kasar suka mika shi ga kananninsa ta wajen uwa don cigaba da kula da shi kafin ta samu sauki.
Adrian Mutu mai kimanin shekara 34 ya taba buga wa kulob din Chelsea kwallo amma an yi masa korar kare ne a shekarar 2004 bayan da aka same shi da yin mu’amala da hodar iblis (cocaine).
dan kwallon wanda ke da mata da yara uku, ya ce “ya kadu matuka a lokacin da ya kalli yadda al’amarin ya kasance a akwatin talabin a gidansa da ke Faransa kuma nan take ya yanke shawarar neman mahukunta su mika masa jaririn don ya cigaba da kula da shi har tsawon rayuwa.
Yanzu haka Mutu yana buga wasan kwallo ne a Faransa a kulob din AC Ajaccio da ke rukunin ’yan dagaji.
dan kwallon ya kara da cewa, “A mafarki Allah Ya aiko min zan tsinci jariri wanda zan mayar da shi nawa, don haka a lokacin da na ga rahoton tsintar wannan jariri a bututun kashi na yi amanna jaririn da na yi mafarki kenan kuma hakan ta sa na yanke shawarar neman a ba ni shi”.
Sai dai dokar kasar Sin ta haramta wa wasu kasashe kimanin 17 izinin mallakar ’yan kasar kuma ciki har da kasar haihuwar Adrian Mutu watau Romaniya. Don haka da wuya kasar Sin ta amince da batun dan kwallon. Hasalima dai tuni mahaifi da mahaifiyar jaririn suka bayyana kuma da wuya su amince a mika dansu ga wani mutum alhali suna raye.