Tsohon dan kwallon Eagles ya rasu

Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) ta bayar da sanarwar mutuwar tsohon dan kwallon tsakiya a kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Mista John Ene Okon.Tsohon dan kwallon ya rasu ne a ranar Talatar da ta gabata a wani asibiti da ke Kalaba.Marigayin ya taba yi wa kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara […]

Tsohon dan kwallon Eagles ya rasu
Tsohon dan kwallon Eagles ya rasu

Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) ta bayar da sanarwar mutuwar tsohon dan kwallon tsakiya a kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Mista John Ene Okon.
Tsohon dan kwallon ya rasu ne a ranar Talatar da ta gabata a wani asibiti da ke Kalaba.
Marigayin ya taba yi wa kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 20 (U-20) wasa a gasar cin kofin duniya da ya gudana a shekarar 1987 sannan ya yi wa Super Eagles wasa a gasar cin kofin Afirka a shekarar 1992 inda Eagles ta gama a matsayi na uku.
Kafin rasuwarsa, shi ne kocin kungiyar kwallon kafa ta Kalaba Robas (Calabar Robers).
Tuni ’yan uwa da abokan arziki suka mika sakon ta’aziyyarsu ga iyalan mamacin ciki har da Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF).
Jama’a da dama sun shaidi mamacin a matsayin mai nuna kwazo da saukin kai musamman a lokacin da yake kwallo.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa