Tsohon dan kwallon Jamus Beckenbauer, ya mutu

Kafin rasuwarsa ya taba lashe kyautar gwarzon Ballon d’Or shekarar 1972 da kuma 1976.

Tsohon dan kwallon Jamus Beckenbauer, ya mutu

Zakaran duniya a  fagen   kwallon kafa a 1974, Franz Beckenbauer  ya mutu yana da shekara 78 a duniya.

Hukumar Kwallon Kafar Jamus (DFB) ce ta sanar hakan a ranar Litinin.

Beckenbauer ya bar kyakyawan tarihi ta fanin kwallon kafa, inda ya samar da ci gaba mai tarin yawa.

Beckenbauer, ya jagoranci Jamus wajen lashe Kofin Duniya a shekarar 1974.

Iyalinsa sun tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Labaran Jamus DPA ya fitar.

“Cikin bakin ciki muna sanar da rasuwar mijina, mahaifinmu, Franz Beckenbauer, ya rasu a kusa da iyalinsa a ranar Lahadi,” in ji sanarwar.

Kafin  rasuwarsa ya taba buga kwallo a kungiyar Bayern Munich da ke Jamus, inda ya zama abun koyi ga matasan ’yan wasan kungiyar.

Ya taba lashe kyautar Gwarzon Ballon d’Or a shekaru 1972 da 1976, sannan ya yi ritaya daga kwallo a 1984 lokacin da yake murza leda a kungiyar New York Cosmos da ke Amurka.

Tuni duniyar kwallo ta shiga jimami da ta’aziyyar fitaccen dan kwallon duniyar.