Tsohon dan majalisar tarayya ya bukaci ’yan Arewa su rika kafa kungiyoyi

Tsohon dan majalisar dokoki ta tarayya mai wakiltar mazabar Iba-dan ta Arewa, Alhaji Abdulwaheed Aderemi Gbede, ya nemi al’ummar Arewa, musamman ’yan kasuwa da masu gudanar da wasu ayyuka a Jihar Oyo, su rika kafa kungiyoyin gamayya domin ita ce hanya mafi sauki da za su kusanci gwamnati wajen samun tallafin da aka saba bayarwa […]

Tsohon dan majalisar tarayya ya bukaci ’yan Arewa su rika kafa kungiyoyi

n shugaba Alin Xanmeri (na huxu daga dama) ke nan tare da Mista Abass Gbede da ya wakilci Abdulwaheed Gbede (a tsakiya) da Hajiya Maikuxi Sulaiman, daya daga cikin wakilai da suka mika kyautuka ga kungiyar ta SAHC a Ibadan.Tsohon dan majalisar dokoki ta tarayya mai wakiltar mazabar Iba-dan ta Arewa, Alhaji Abdulwaheed Aderemi Gbede, ya nemi al’ummar Arewa, musamman ’yan kasuwa da masu gudanar da wasu ayyuka a Jihar Oyo, su rika kafa kungiyoyin gamayya domin ita ce hanya mafi sauki da za su kusanci gwamnati wajen samun tallafin da aka saba bayarwa ga irin wadannan kungiyoyi domin bunkasa harkokinsu.
Alhaji Abdulwaheed A. Gbede ya yi wannan tsokaci ne cikin jawabin da wakilinsa, Mista Abass Gbede ya karanta a lokacin da yake mika kyautar janareta da wasu kayayyakin bukatu ga kungiyar Gamayyar Hausawa mazauna Jihar Oyo (Society for the Adbansement of Hausa Community in Oyo State -SAHC) a ofishinta da ke kasuwar Bodija, a Ibadan.
Ya ce, bincike ya nuna cewa gamayyar kungiyoyi domin tafiya da murya daya wajen isar da manufofi ga mahukunta da jama’a, ya taimaka wajen kusantar hukuma a kasashen duniya da suka ci gaba da suka tsoma kungiyoyin cikin ayyukansu. Ya nemi shugabannin Hausawan su rika tuntubar ofishinsa domin samun shawarwari da za su taimake su.
Tun da farko sai da Kakakin kungiyar, Alhaji Yahya Abdullahi Maizabura ya karanto tarihin kafuwar kungiyar da irin gwagwar-mayar da ta yi kafin ta kai ga wannan matsayi, musamman wajen gina babbar sakatariyar da aka kashe fiye da Naira miliyan 5 kan ta.
Cikin jawabin maraba da Shugaban kungiyar, Alhaji Alin danmeri ya karanta, ya ce duk da yake kungiyar tasu ta ’yan Arewa ce kawai, “Amma kofarmu a bude take ga dukkan kabilu da suke sha’awar shigowa cikinmu domin duka jirgi daya ya kwaso mu, babu bambancin kabila ko addini a cikinmu, muna bukatar samo hanyoyin bunkasa harkokinmu ne”.