Tsohon dan qwallon Pillars ya mutu a lokacin da yake qwallo
Wani abu mai kama da al’mara ya faru a qarshen makon jiya bayan tsohon dan qwallon Kano Pillars da kuma Heartland na Owerri Abdul Haruna ya yanke jiki ya fadi a lokacin da yake tafiya da qwallo a ranar Lahadin da ta wuce.Al’amarin ya faru ne a lokacin da Haruna mai kimanin shekara 27 yake […]

Wani abu mai kama da al’mara ya faru a qarshen makon jiya bayan tsohon dan qwallon Kano Pillars da kuma Heartland na Owerri Abdul Haruna ya yanke jiki ya fadi a lokacin da yake tafiya da qwallo a ranar Lahadin da ta wuce.
Al’amarin ya faru ne a lokacin da Haruna mai kimanin shekara 27 yake buga wa kulob din Kano Professionals a wani wasan sada zumunta da ya gudana a Kano.
A lokacin da yake bayyana labarin mutuwar dan qwallon, mai magana da yawun qungiyar qwallon qafa ta Kano Pillars Idris Malikawa ya bayyana kaduwarsa da kuma daukacin ’yan qwallon Pillars da wadanda suka halarci filin wasan a bisa faruwar wannan al’amari. “Ya rasu ne a lokacin da yake tafiya da qwallo kuma babu wanda ya taba shi balle a ce sun yi arangama ne, kuma a lokacin yana yi wa zababbun ’yan qwallon Kano Professionals ne wadanda suke karawa da wani kulob da ke rukunin ’yan dagaji a wasan sada zumunta”.
“Bayan ya fadi ne sai aka garzaya da shi asibiti amma kafin likitoci su kai masa dauki rai ya yi halinsa,” inji Malikawa.
Tuni aka yi jana’izar marigayin a ranar Litinin da ta wuce a Kano kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Marigayin ya rasu ya bar matarsa mai suna Surayya da da daya. Kuma ya yi aure ne a shekarar 2012.
Kafin rasuwarsa yana yin qwallo ne a bietnam da wani kulob mai suna Song Lam Ngbe kuma ya dawo Najeriya hutu ne kafin ya koma a watan Janairu mai zuwa sai rai ya yi halinsa.