Tsohon dan takarar Gwamnan Sakkwato ya ce akwai hadin baki a sace mahaifiyarsa

daya daga cikin wadanda suka tsaya takarar Gwamnan Jihar Sakkwato a karkashin Jam’iyyar APC a zaben da ya gabata, Alhaji Yusha’u Ahmad Kebbe ya yin zargin cewa da batagarin kauyensu aka hada baki aka sace tare da yin garkuwa da mahaifiyarsa, inda sai da ya biya fansa ta miliyoyin Naira aka sako ta.Alhaji Yusha’u Kebbe […]

Tsohon dan takarar Gwamnan Sakkwato ya ce akwai hadin baki a sace mahaifiyarsa
Tsohon dan takarar Gwamnan Sakkwato ya ce akwai hadin baki a sace mahaifiyarsa

daya daga cikin wadanda suka tsaya takarar Gwamnan Jihar Sakkwato a karkashin Jam’iyyar APC a zaben da ya gabata, Alhaji Yusha’u Ahmad Kebbe ya yin zargin cewa da batagarin kauyensu aka hada baki aka sace tare da yin garkuwa da mahaifiyarsa, inda sai da ya biya fansa ta miliyoyin Naira aka sako ta.
Alhaji Yusha’u Kebbe wanda fitaccen dan siyasa ne a Jihar Sakkwato ya bayyana wa taron manema labarai da ya kira a Cibiyar ’Yan jarida ta Sakkwato da ke Dogondaji cewa: “An hada baki da batagarin kauyenmu ne aka sace mahaifiyata idan aka yi la’akari da yadda aka dauke ta, bayan Sallar Magariba a ranar Asabar da ta wuce, inda wasu mutane suka zo da bindigogi har cikin gidan da mahaifiya Fatima Muhammad take zaune, daya daga cikin mutanen ya umarci wata da ke kusa da mahaifiyata, cewa ta tashi su tafi sai dayan ya ce masa ba ita ba ce, wannan ce ta gefenta. Yaya aka yi ya san mahaifiyata tun da ba ta yawo in ba dan gari ba ne? Sun fito da ita suka bace a garin ba a san inda suka shiga ba, bayan lokaci kadan suka kira mu suka gaya mana bukatarsu ta mu ba su miliyoyin Naira.”
Alhaji Yusha’u Kebbe wanda ke bayyana hakan kwana daya da sako mahaifiyarsa, ya kara da cewa wannan harka ta siyasa ce don a kan haka da aka yi an yi ta yada karya da kazafi a kansa na abubuwan da bai sansu ba, sai dai ya ce hakan ba zai sa gwiwarsa ta yi sanyi ba wajen kawowa jama’ar canji mai amfani da dorewa.
Ya gode wa manema labarai kan yadda suka yayata lamarin inda ya ce ba don kwazonsu ba mutane ba za su san abin da ya faru gare shi ba musamman jama’ar jihar da abokansa da ke wajen Sakkwato. “Mun gode Allah jiya (ranar Litinin) da misalin karfe 2:00 na dare wadanda suka yi garkuwa da mahaifiyata suka sako ta, ta kira muka je muka dauko ta a Gadar Zema kusa  ga daki-Takwas a Jihar Zamfara a halin yanzu tana asibiti don duba lafiyarta saboda tana fama da ciwon hawan jini. Kuma a kwana ukun da ta shafe a wurinsu ta ce ba zagi ba duka amma wurin da aka a jiye ta yana da matukar kazanta. Ina son in gaya wa mutanen kauyenmu da ke fadar magana marar kyau a kaina cewa wai na saci kudin gwamnati a lokacin ina dan majalisa kuma kan haka ne wai na kwashi iyalina zuwa kasar Dubai na bar mahaifiyata, da mutanen suka zo ba su same ni ba sai kawai suka tafi da ita, wannan abin damuwa ne mutanenka su gayyaci batagari don musgana wa wani, wanda zai taimaka a yi wani aiki mai muni, shi ma batagari ne,” inji shi.
Ya tabbatar da cea sun bayar da kudin da masu garkuwar suka nema inda ya yi zargin cewa mutanen suna da wani shiri a gaba, don haka ya yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi tsaye wajen kawar da batagari don suna barazana ga harkar tsaron Najeriya.
Kebbe ya gode wa Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da tsofaffin gwamnonin jihar Alhaji Attahiru Bafarawa da Alhaji Aliyu Wamakko da sauran mutanen da suka taimaka wajen ganin an kubutar da mahaifiyarsa.
Aminiya ta samu labarin cewa an biya kudin fansa har Naira miliyan 50, kafin sako dattijuwar.